Kotun Koli ta kori karar da Jam’iyyyar PDP ta daukaka zuwa gabanta na neman kotun ta soke takarar Bola Bola Tinubu da Kashim Shettima a matsayin dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa a Jam’iyyar APC a zaben 2023 da ya gabata.
Kotun ta yi fatali da karar da PDP ta daukaka ne da cewa babbar jam’iyyar adawar ba ta da hurumin shigar da karar ko tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar APC, wadda sha’anin cikin gidanta ne tsayar da ’yan takararta.
PDP ta daukaka karar ne ta hannun lauyanta Mike Ozekhome (SAN), cewa Shettima ya tsaya takarar kujerar Sanatan Borno a Tsakiya da kuma mataimakin shugaban kasa na APC a lokaci guda.
Idan za a iya tunawa a baya Babbar Kotun Tarayya ta kori karar har ta ci jam’iyyar PDP tarar Naira miliyan biyar, amma jam’iyyar ta daukaka karar zuwa Kotun Koli.
Alkalan kotun su biyar sun kori karar na PDP ne a safiyar Juma’a, kwana biyu kafin ranar rantsar da Tinubu da Shettima a ranar Litinin.
A ranar Alhamis aka kaddamar da bukukuwan mika musu mulki, inda shugaba Buhari ya mika wa Tinubu kundin bayanan ayyukan gwamnati, sannan ya karrama shi da lambar girmamawa ta kasa mafi daraja ta GCFR, wadda ake ba wa shugabannin kasa.
An kuma karrama Shettima da lambar GCON, wadda ke biye da GCFR, a matsayin matamakin shugaban kasa mai jiran gado.