Daily Trust ta tsaya kan bakanta game da rahoton rage darajar Naira

0
156

Fitacciyar Jaridar da ake wallafa a Najeriya, ‘Daily Trust’ ta ce tana nan akan bakanta dangane da labarin da ta wallafa a game da matakin babban bankin CBN na rage darajar Naira.

A ranar Alhamis jaridar ta ruwaito cewar bankin Najeriyar ya rage darajar kudin kasar daga naira 465 zuwa 631 akan kowace dalar Amurka guda.

Sai dai bayan jim kadan bayan wallafa labarin, bankin na CBN ya fitar da sanarwar da ke musanta rahoton.

Tuni dai jaridar ta ‘Daily Trust’ ta mayar da martanin cewar tana da cikakkiyar hujja daga mutanen da suka sayi dalar akan sabon farashin na naira 631, tare da kalubalantar babban bankin Najeriyar akan ya bayyana ta sa hujjar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here