Kungiyar IFC ta zuba jarin Dala miliyan 500 a kamfanin BUA

0
99

Kungiyar masu zuba jari ta duniya ta IFC ta sanar da zuba jari na Dala miliyan 500 wanda shine mafi girma a yankin arewacin Najeriya domin hada kai da kuma taimakawa kamfanin BUA bunkasa aikinsa na samar da wadataccen siminti da kuma gina wasu sabbin sassa wanda zai samar da ayyukan yi dubu 12 a ciki da wajensa.

Kamfanin wanda ke cikin kungiyoyin Bankin Duniya ya sanar da wannan hadin gwuiwar ne a wajen taron shugabannin kamfanoni masu zaman kansu dake gudana a Abidjan, inda yake cewa matakin zai baiwa BUA damar fadada kamfanin simintinsa dake Sokoto tare da kuma samar da wutar lantarki ta hanyar hasken rana.

Sanarwar IFC tace kamfanin simintin zai dinga samar da tan 300 na siminiti kowacce shekara idan an kammala fadada shi, matakin da zai taimakawa kasuwannin Najeriya da Nijar da kuma Burkina Faso.

Sanya wadannan kudade na Dala miliyan 500 zai kunshi Dala miliyan 160 daga asusun IFC da Dala miliyan 94.5 rance daga MCPP da kuma Dala miliyan 245 daga hukumomi daban daban da suka hada Bankin Raya kasashen Afirka na AfDB wanda ya zuba Dala miliyan 100 da AFC da ya bada Dala miliyan 100 sai kuma Hukumar zuba jari ta Jamus da ta zuba Dala miliyan 45.

Shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabi’u ya bayyana matukar farin cikinsa da wannan nasarar da suka samu ta Dala miliyan 500 da zasu bunkasa kamfanin simintinsu da kuma samar da makamashi a yankin arewacin Najeriya.

Rabi’u yace wannan ci gaba da suka samu zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da kuma bunkasa kayayyakin more rayuwa a Najeriya da kasashen yankin Sahel.

Yayin bayyana farin cikin nasa, shugaban kamfanin BUA ya kuma ce matakin zai taimaka musu wajen karkata akalar amfani da makamashin da baya gurbata muhalli.

Babban Daraktan kungiyar IFC da ya tattaro kudaden da za’a sanya a kamfanin BUAn, Mukhtar Diop yace suna masu matukar farin ciki da wannan hadin gwuiwar wanda zai bunkasa masana’antu da kirkiro ayyukan yi da kuma bunkasa tattalin arzikin yankin arewacin Najeriya. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here