Uwargidan gwamnan Abia ta ziyarci yan matan masana’antar jarirai da aka ceto

0
109

Uwargidan gwamnan jihar Abia, Misis Priscilla Otti a ranar Talata ta kai ziyarar bazata ga wasu ‘yan mata masu juna biyu 21, wadanda aka ceto daga masana’antar jarirai da ke Umunkpei, Nvosi, a karamar hukumar Isialangwa ta Kudu tare da bada tabbacin daukar matakin da ya dace cikin gaggawa dauka don ceto rayuwar su.

Misis Otti, wacce ta bayyana bakin ciki da takaici kan lamarin ta bayyana hakan a matsayin abin takaici, duk da haka, gwamnati na bayar da kulawa na wucin gadi ga ‘yan matan.

Ta yi nadama kan yadda ake aiwatar da irin wannan mummunan aiki a jihar Abia, ta kuma ba da tabbacin gwamnati za ta hada hannu da  coci-coci, da sauran masu ruwa da tsaki domin ba da taimakon da ya dace domin kula da kananan yara mata da kananan yara a jihar.

Da yake jawabi tun da farko, Provost, Madonna College of Health Technology, Olokoro, inda ake kula da ‘yan matan, Rev. Father Christian Anokwuru ya bayyana yadda gwamnati ta kai fursunonin sashen haihuwa na kwalejin lafiya domin kula da su.

Ya bayyana cewa ‘yan matan da adadinsu ya kai 20 suna dauke da juna biyu yayin da aka gudanar da bincike da gwaji a kansu, inda ya ce daya daga cikinsu ta haifi jariri. Ya kuma tabbatar wa uwargidan gwamnan cewa za a ba su abinci yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here