Rundunar sojin Nijeriya na koya wa dakarunta darasi kan yakin basasa

0
120

Rundunar sojin Nijeriya ta gudanar da taro ga dakarunta da zummar fahimtar da su illoli da kuma darussan da ke tattare da yakin basasa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Manjo Hashimu Sa’ad Abdullahi ya fitar ta ce Kwalejin Koyar da Yaki ta kasar, ta shirya taro ga dakarunta na kwas na 7 kan bukatar waiwaye game da yakin basasa da aka yi a kasar.

Sanarwar ta ambato babban hafsan sojin kasa na Nijeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya yana jaddada “muhimmancin yin nazari kan Yakin Basasar Nijeriya saboda akwai manya-manyan darussa da za su taimaka wurin magance matsalolin rashin tsaro da kasar ke fuskanta.”

Ya ce yanayin rashin tsaro na yanzu yana da sarkakiya da hatsari da kuma rashin tabbas.

“Fahimtar tarihin kasa zai taimaka a gamsu da yadda aka kwashe shekara da shekaru wurin gina manyan ababen more rayuwa, wadanda ana iya rusawa a lokaci kankane, kuma hakan yana da muhimmanci wajen ci-gaban kasa,” in ji sanarwar sojin Nijeriya.

An gudanar da yakin basasar Nijeriya ne daga 1967 zuwa 1970 sakamakon yunkurin da Gabashin kasar ya yin a ballewa don kafa kasar Biafra.Hoto/Rundunar Sojin Kasa ta Nijeriya

An gudanar da yakin basasar Nijeriya ne daga 1967 zuwa 1970 sakamakon yunkurin da Gabashin kasar ya yin a ballewa don kafa kasar Biafra.

Lamarin ya yi sanadin mutuwar miliyoyin mutane da lalacewar ababen more rayuwa.

A shekarun baya bayan wasu ‘yan kabilar Igbo karkashin jagorancin Nnamdi Kanu sun farfado da wannan batu inda har yanzu suke tayar da kayar baya, ko da yake tuni gwamnati ta tsare Mr Kanu bisa zargin ta’addanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here