Attajirin Qatar ya gabatar da tayin karshen kan sayen Manchester United

0
130

Hamshakin attajirin kasar Qatar Shiekh Jassim bin Hamad Al Thani, ya sake gabatar da tayin sayen kungiyar Manchester United daga iyalan Glazer.

Wani makusancin attajiirin ya ce tayin shi ne karo na biyar, kuma na karshe da Sheikh Jassim zai yi kan aniyarsa ta sayen United, kokarin da ya rika yi tun daga shekarar bara.

A cewar attajirin daga ranar Juma’a ba zai sake shiga wata tattauna akan sayen kungiyar da ke gasar Premier Ingila ba.

Tun cikin watan Nuwamban bara iyalan Glazer suka bayyana aniyarsu ta sayar da Manchester United, wadda suka saya akan farashin fam miliyan 790 a shekarar 2005, kungiyar da a yanzu darajarta ta kai Fam biliyan 5 zuwa 6.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here