An hana amfani da jiniya ba bisa ka’ida ba a Kano

0
127

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya ta haramta amfani da jiniya ga mutanen da ba hukuma ba ne su da ma wadanda suke hukuma din a cikin awannin da aka haramta hakan.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar a ranar Alhamis, inda ta ce za a kama duk wanda ya taka wannan doka tare da gurfanar da shi a gaban shari’a.

“Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta fahimci yadda mutanen da ba hukuma ba ne da ma wadanda hukumar ne amma suke amfani da jiniya a kowane lokaci ba tare da bukatar hakan ta taso ba,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ci gaba inda ta fayyace irin motoci da mutanen da ya kamata su dinga amfani da jiniya a cikin al’umma, kamar su motocin asibiti na gaggawa, “kuma ko su ma akwai sharuddai da lokutan da bai kamata su yi amfani da jiniyar ba.

“A ka’ida ana kunna jiniya ne kawai daga karfe 6 na safiya zuwa 6 na yamma,” a cewar sanarwar.

Rundunar ta kuma gargadi al’umma da cewa ya kamata su fahimci jiniya na jawo hayaniya da damun marasa lafiya da kuma a wasu lokutan zama salon a cin zarafin mutane.

A don haka ne Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar ya ce tuni aka bai wa jami’ai umarnin sa ido da gabatar da duk wanda aka kama da karya dokar ga hukuma.

Kazalika hukumar ‘yan sandan ta ce za a fara kama duk wanda aka kama ya rufe lambar abin hawansa kuma za a gabatar da shi ga shari’a don tuhumarsa a kan wannan laifin.

A karshe, rundunar ‘yan sandan ta gode wa al’ummar jihar bisa goyon baya da hadin kan da ta ce suna ba ta, sannan ta shawarci mutane da su guji tukin ganganci da tabbatar da bin doka da oda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here