Tinubu ya gana da jagoran NNPP a Abuja

0
141

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, na ganawa da jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a fadar Villa da ke Abuja.

Kwankwaso wanda ya kasance a matsayin na hudu, a zaben shugabancin kasar da aka yi a watan Fabrairu, shine ya wakilci jam’iyyar ta NNPP.

Shine dan takarar shugabancin kasar na farko da ya ziyarci sabon shugaban a Aso Rock.

A watan jiya ne dai Kwankwaso ya gana da Tinubu a birnin Paris na kasar Faransa, inda suka dauki tsawon sa’o’I hudu suna tattaunawa kan batutuwan da suka shafi kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here