Mutumin da ya yi kwana 100 a karkashin ruwa bai ga rana ba

0
120

Wani malamin jami’a ya kwashe fiye da kwana 100 a karkashin ruwa bayan da ya yi ninkaya a cikin ruwan kuma ya daga fuskarsa ya kalli rana a karon farko tun ranar 1 ga watan Maris.

Dokta Joseph Dituri ya kafa sabon tarihi ne a ranar Juma’a, bayan ya kasance a karkashin ruwa a wani wurin hutawa da ke cikin ruwa mai suna Jules’ Undersea Lodge, wanda yake kasan ruwa – mai zurfin mita 9.14 a kogin Key Largo da ke jihar Florida.

Mai binciken na bangaren kiwon lafiya ya wuce wadanda suka gabace shi – wasu farfesoshi biyu daga jihar Tennessee wadanda suka yi kwana 73 da awa biyu da minti 34 a karkashin ruwa a wannan kogi a shekarar 2014.

Bajintar da Dituri ya kafa ta dara wadda Jessica Fain da Bruce Cantrell suka kafa, wadanda suka yi kwana 73 a cikin kogin.

“Ban damu da batun kafa bajintar ba,” in ji Dituri.

“Na fi damuwa da nuna tsawon lokacin da dan Adam zai iya jurewa a karkashin ruwa da yadda aka killace shi a wuri daya da yadda yake iya jurewa mullali mara dadi.”

Dituri, wanda kuma ake kira da “Dr Deep Sea,” wato Dokta na Karkashin Ruwa, yana koyarwa ne a Jami’ar South Florida kuma yana da digiri na uku a fannin ilimin kimiyyar sinadaran jikin jiki wato Biomedical Engineering kuma sojan ruwa ne mai ritaya.

Kundin Bajinta na Guiness World Records sun bayyana sunan Dituri wanda yake rike da bajintar a shafinsu na intanet bayan da ya yi kwana 74 a karkashin ruwa a watan jiya.

Cibiyar da ke kula da albarkatun ruwa wato The Marine Resources Development Foundation, wadda ta mallaki ruwan, za ta bukaci kundin ya sanya sunan Dituri dangane da bajintar kwana 100 a kasan ruwa da ya yi, kamar yadda shugabanta Ian Koblick ya bayyana.

Shirin da aka sanyawa sunan Project Neptune 100

An yi wa abin da Dituri ya yi lakabi da sunan Project Neptune 100, kuma cibiyar ce ta dauki nauyin aikin.

Ba kamar sojojin ruwa ba, wadanda suke samar da yanayi a kasar ruwan wanda ya yi kama da na tudu, Dituri bai yi amfani da irin wadannan yanayin da aka samar ba.

Shirin an tsara shi ne don a fahimci yadda jikin dan Adam da ruhinsa yake tasirantuwa da muhalli mai tattare da kalubale kuma an tsara shi ne saboda ya amfanar da masu bincike da ‘yan sama jannati a aikace-aikacensu na gaba.

Lokacin da ya yi wata uku da kwana tara da ya kwashe a kasan ruwa, Dituri ya rika yin gwaje-gwaje da aune-aune a kullum kan yadda jikinsa yake sauyawa a tsawon lokacin.

Kuma ya gana da dubban dalibai daga kasashe 12 ta intanet, ya kuma koyar da darussa a Jami’ar South Florida kuma ya karbi bakuncin fiye da mutum 60 wadanda suka kawo masa ziyara.

“Abin da ya fi komai ba ni farin ciki shi ne ganawa da dalibai kusan 5,000 kuma suka nuna damuwarsu kan karewa da alkinta muhallin kasan ruwa,” in ji Dituri.

An shirya Dituri zai gabatar da abin da binciken aikinsa da aka yi wa lakabi da Project Neptune 100 ya gano a watan Nuwamba a wani taron fannin likitanci na World Extreme Medicine Conference a kasar Scotland.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here