Godswill Akpabio: Abubuwa 5 game da sabon shugaban majalisar dattawan Najeriya

0
98

An zabi Sanata Godswill Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa ta 10.

Akpabio wanda tsohon gwamnan Jihar Akwa Ibom kuma dan majalisa daga shiyyar Akwa Ibom ta Arewa Maso Yamma, ya lashe zaben bayan samun kuri’u 63, inda ya doke abokin hamayyarsa, Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan Jihar Zamfara, wanda ya samu kuri’u 46.

Babban magatakardar majalisar, Sani Tambuwal ne ya sanar da sakamakon.

A cewarsa, Sanatoci 107 ne suka kada kuri’a.

Abubuwa biyar game da sabon shugaban Majalisar Dattawa:

1. An haife shi a ranar 9 ga watan Disamba, 1962. Ya girma a hannun mahaifiyarsa bayan rasuwar mahaifinsa yana karami.

2. Ya halarci Jami’ar Kalaba da ke Jihar Kuros Riba, inda ya karanci fannin shari’a.

3. Ya yi aiki daban-daban kama daga malamin makaranta har zuwa matakin manajan kamfani.

4. A 2002, Gwamna Obong Victor Attah na lokacin a Jihar Akwa Ibom ya nada shi Kwamishinan Man Fetur da Albarkatun Kasa. A tsakanin 2002 zuwa 2006, ya yi aiki a matsayin kwamishina a ma’aikatu uku: Man Fetur da albarkatun kasa, kananan hukumomi da harkokin masarautu da kasa da gidaje.

A 2006, ya yi sha’awar tsayawa takarar gwamnan Jihar Akwa Ibom, ya doke wasu ‘yan takara 57 a zaben fid-da-gwani a jam’iyyar PDP.

An zabe shi Gwamna a 2007. An sake zabar shi a karo na biyu a 2011.

A 2013 ne aka zabe shi shugaban sabuwar kungiyar gwamnonin PDP. A 2015 ya tsaya takarar Sanata, kuma ya lashe zaben.

5. EFCC ta binciki Akpabio kan zargin karkatar da sama da Naira biliyan 100 daga Jihar Akwa Ibom a lokacin da yake gwamnan jihar daga 2007 zuwa 2015.

Kazalika, a watan Mayun 2020 ne ‘yan majalisar wakilai suka gayyaci Akpabio kan zargin almundahanar Naira biliyan 40.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here