Hotuna: Gini ya kashe mai dibar ganima a Kano

0
89

Gini ya danne mutane da dama da ake zargin masu dibar ganimar rodina da saura kayan gini ne a tsohon otal din Daula da ke Kano.

Ginin dai na daya daga cikin wadanda Gwamnatin Jihar Kano ta rusa bisa dalilin cewa tana kokarin kwato filayen gwamnati da aka cefanar ba bisa ka’ida ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutum daya ya rasa ransa, wasu uku kuma an ceto su da rai, wasu kuma har yanzu ana ci gaba da aikin ceto su.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 2:30 na rana, lokacin da mutanen ke kokarin dibar rodi daga cikin ginin.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf, wanda ya yi magana da wakilinmu a wajen, ya ce yanzu haka jami’ansu sun sami nasarar ceto mutum uku da ransu.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, ana zargin akwai karin wasu mutum biyu ko fiya da haka a cikin ginin.

Ga wasu daga cikin hotunan aikin ceton:

Masu dibar ganima

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here