Rashin tsaro: Gwamnan Zamfara ya nemi taimakon babban hafsin tsaron kasa

0
114

Dangane da matsalar tsaro a jiharsa, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya nemi tallafin sojoji domin shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar jihar.

Gwamna Lawal ya nemi goyon bayan soji a jihar, a ziyarar da ya kai wa babban hafsan tsaron kasa (CDS), Janar Lucky Irabor, a hedikwatar tsaro da ke Abuja.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya aike wa LEADERSHIP, ta bayyana cewa ziyarar na daya daga cikin kokarin gwamna Lawal na wanzar da zaman lafiya da tsaro a jihar Zamfara.

“Gwamna Lawal ya ziyarci hedikwatar tsaro ne domin ya yaba da kokarin da sojoji ke yi a yaki da ‘yan bindiga a Jihar Zamfara.

“Ya yi ganawar sirri da babban hafsan hafsoshin tsaron kasar nan, Janar Lucky Irabor, domin tattauna muhimman batutuwan tsaro da kuma hanyar da za a bi.

“Kudirin gwamnatinmu ne ta amince da alhakin da ya rataya a wuyan gwamnatin tarayya kan harkokin tsaron cikin gida, wanda ya hada da hada gwiwa da sojoji.

“Gwamnan ya damu da rashin tsaro da ake fama da shi a wasu yankunan Jihar Zamfara, don haka ya hada gwiwa da duk masu ruwa da tsaki a cikin hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya,” in ji Idris.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here