An koma karatu a jami’ar Ahmadu Bello

0
138

Majalisar Gudanarwa ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ta sanar da sake bude makarantar domin ci gaba da gudanar karatun zango na biyu.

A wata sanarwa da jami’ar ta buga a mujallarta da ke fita lokaci zuwa lokaci, ta ce sakamakon taron gaggawa karo na 523 da majalisar ta gudanar a ranar Juma’a 16 ga watan Yuni 2023, an bukaci daukacin dalibai da su dawo domin ci gaba da karatu daga ranar Litinin, 19 ga watan Yuni 2023.

Aminiya ta ruwaito cewa, daliban jami’ar sun shafe tsawon wata guda suna zaman gida sakamakon yanke wutar lantarki da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kaduna KEDCO ta yi a jami’ar.

Binciken da wakilin mu ya gudanar, ya tabbatar da dawowar wutar lantarkin, lamarin da ake zargin shi ne ya sa aka yi wa daliban kiranyen dawowa jami’ar.

Sai dai takardar sanarwar bata fayyace ko hukumar jami’ar ta samu nasarar biyan kudaden wutar lantarkin da ake binta ko kuma irin matsayar da suka samu da hukumar samar da wutar lantarkin don kaucewa faruwar irin haka a nan gaba.

Yanzu dai ana sa ran daukacin dalibai za su dawo a ranar Litinin don ci gaba da gudanar da karatu bisa tsarin yadda aka yi wa jadawalin karatun kwaskwarima

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here