Ana binciken ‘yan sandan da suka karbi Naira 40,000 daga hannun wasu fasinja

0
129

Wani mai amfani da shafin Twitter @LifeOfNapaul ya zargi wasu ‘yansanda da karbar Naira 40,000 daga wurinsa da wasu mutum uku a jihar Ribas.

Da yake bayyana irin halin da ya tsinci kansa a wani sako inda ya buya ya wallafa a shafinsa na Twitter a yammacin ranar Lahadi, mutumin ya ce ya hau motar haya ce akan hanyarsa ta zuwa Fatakwal, suna cikin tafiya ‘yansandan suka tsayar da motar suka fara bincikensa da wasu fasinjoji uku bisa zarginsu da aikata laifi.

Da yake lura da cewa ’yansandan ba su ga wani abu da ya shafi laifuka ba, sai  ‘yansandan suka bukaci Naira 50,000 wato shi ya ba da Naira 20,000 sauran abokan tafiyarsa kuma su ba da Naira 10,000 kowannensu kafin a bar su su ci gaba da tafiya.

Rubutun nasa ya ce, “Na gaji da irin wannan hali na ‘yansand, saboda irin wannan ta taba faruwa da ni aka kai ni ofishin ’yan sanda, aka hada ni da masu laifi kamar mai laifi, saboda kawai na ga ina amfani da wayar iPhone.

“ Gashi yau (Lahadi) a kan hanyata ta zuwa Fatakwal a cikin motar haya an sake tar ni, aka ce mu dakata aka fito da mu aka bincike ni, aka bude hirar da na yi na WhatsApp daya bayan daya, da kowacce manhaja dake kan wayata aka bincke ba su samu komai na laifi ba.

“Duk da hakan dai suka ce ba za su bar mu mu tafi sai ba da wani abu, mu hudu ne maza kawai a cikin matar kirar Sienna, sauran mata ne. Sai suka ce direban ya bar mu a wurin amma na yi ta rokon direban ya tsaya.”

Wanda abin ya shafa ya ce an shafe sama da sa’a guda ana ganar da muhawara, inda ya ce a lokacin da ya yi yunkurin neman hadin kan ‘yansandan domin sasanta lamarin cikin lumana, kawai sai suka buga masa ankwa a hannu.

Ya rubuta, “Dan uwa, ni fa ba mai laifi ba ne, sun ce suna tuhuma ta ne, na yi ta tambayar ‘ta yaya?’ A lokacin na fusata sosai.

Jami’an sun nemi a ba su Naira 50,000, daga karshe dai kowannenmu ya biya Naira Naira dubu 10, suka raba kudin kowannen su ya dauki Naira dubu 10. Abin da ya bani dariya shi ne wadannan da ake kira da jami’an tsaro sai ga su sun buge da kirga kudin da suka a wurin fasinja a gaban mutane.

“Asusun da na aika da kudin, lambar mace ce kuma na bincika Facebook na gano tana zaune a Abuja. Ban sami sunayensu ba, Hilud din da suka yi amfani da shi ba ta jami’in ‘yansandan Nijeriya ba ce kuma gaba daya ma motar ba ta da lamba.”

Wanda aka karbi kudin nasu ya makala hoton daya daga cikin ‘yansandan da ake zargi da karbar kudin a rubutun nasa.

Da yake mayar da martani, kwamandan rundunar ‘yansandan Jihar Ribas, a wani sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, @RibersPoliceNG, ta ce kwamishinan ‘yansandan jihar, Nwonyi Emeka, ya yi Allah wadai da wannan hali da ‘yansandan suka nuna.

“Kwamishanan ‘yansandan da muke da shi a Jihar Ribas ba shi da wata masaniya a kan irin wannan abin kunya da wadannan jami’ai ke yi, sannan ya sha alwashin gano jami’in tare da gurfanar da su gaban kuliya domin fuskantar hukuncin ladabtarwa, kuma ya yi alkawarin mayar muku da kudadenku,” in ji rundunar ‘yansandan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here