Matar da ta zana shatale-talen da gwamnatin Kano ta rusa ta magantu

0
236

Wacce ta zana shatale-talen kofar gidan gwamnatin Jihar Kano ta bayyana yadda ta ji a lokacin da ta samu labarin rushe ginin da ta kirkira.

Malama Kaltume Bulama Gana, shahararriyar mai sana’ar zane-zane wacce kuma ta zana ginin shatale-talen da sabuwar gwamnatin Kano ta rushe a tsakar daren Laraba ta nuna alhinin rusa ginin na tarihi.

A hirarta da wakilinmu ta wayar tarho, ta bayyana yadda ‘yan uwa da dangi da kuma masoya daga ciki da kuma wajen Kano suka rika bugo mata waya na jajen rusa ginin da gwamnatin jihar ta yi wanda hakan ya shafe tarihin cikar jihar 50.

“Tun safe na ke ta amsa wayar jama’a ana yi min jajen rushe ginin, abin har ya isheni” inji Malama Kaltume

Wakilinmu wanda ya ce da kyar ya samu layin wayarta a daren Alhamis, ya kuma ce da kyar suka yi magana saboda yawan katsewar layin watakila saboda rashin kyau ko kuma na yawan wadanda ke kan layin son magana da ita.

Kwararriyar mai zane-zanen ita ta samar da taswirar ginin shatale-talen ne a wata gasa da gwamnatin jihar ta saka ne a lokacin cikar jihar Kano shekaru 50 da kafuwa a shekarar 2017

A inda taswirar zanen nata ya zo na daya a gasar, aka kuma dauka aka gina domin tunawa da wannan lokaci na tarihi.

Ginin mai suna ‘The Golden Gate’ an gudanar da kasaitaccen biki na kaddamar da shi duk da korafe-korafen da aka yi ta yi na zunzurutun kudin da gwamnatin Gnduje ta ce ta kashe wajen ginawa da kuma kawata shi.

Sannan a bikin ta kuma ba Malama Kaltume kyautar karramawa na wannan bajintar a gaban dubban jama’ar da suka halarta daga cikin da kuma wajen jihar.

Duk da cewa abin ya wuce amma har yanzu ana danganta ginin da ita, kasancewarta mace ta farko da ta yi wannan abin a-zo-a-gani musamman a fannin da maza ne suka yi fice a cikinsa.

Ko a farkon shekarar 2023, sai da kungiyar masu gashin burodi ta kasa reshen Jihar Kano a bikinsu na shekara-shekara suka gasa kek mai girman gaske da siffar kofar don karramata.

Ginin shatale-talen na kofar gidan gwamnatin Kano da aka rushe shi ne na uku a jerin gine-ginen da gwamnatoci suka yi na musamman don murnar tunawa da cikar jihar wasu shekaru da kirkiro ta.

A shatale-talen Gidan Murtala a kofar Nassarawa shi aka fara yi a lokacin da Kano ta cika shekaru 20 da kafuwa.

An yi na kan rawun din makarantar Takanikal da ke kan titin Zariya nesa kadan da na farko da jihar ta cika shekaru 25, aka kuma lakaba masa suna ‘Silver Jubilee’.

Cikon na uku shi ne na kofar gidan gwamnati wanda aka yi a lokacin da ta cika shekaru 50, aka kuma lakaba masa ‘Golden Jubilee’

Na farkon guda biyu duk an sake gina su a gefe a lokacin da aka rushe su saboda aikin gadar sama da aka yi.

Rushe ginin ya janyo cece-ku-ce a ciki da kuma wajen jihar Kano, yayin da wasu ke suka wasu musamman masu goyon bayan gwamnati suna kare yin hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here