Wasu mutane a tarihi sun yi kokarin sace Manzon Allah (SAW) a kabarinsa, amma haka bai yiwu ba sakamakon dauki da Allah Ya kawo ta hanyar tona asirinsu cikin wani yanayi na ban mamaki.
A cikin Karni na 16 zuwa na 17 wasu Larabawa masu wata irin akida sun yi kokarin sace Manzon Allah (SAW) da niyyar mayar da shi inda suke.
Don cim ma wannan buri sai aka turo wasu mutane da kudi mai yawa irin na wancan lokaci, inda suka zo garin Madina suka gina gida, suka kuma shiga hidimar ciyar da mutane abinci da sauran hadindimu na sa-kai.
Ana haka labarinsu ya watsu a ko’ina ciki da wajen Madina na cewa, ga wasu mutane sun sauka a garin da wani aiki na ciyar da jama’a abinci da kuma sauran ayyuka na taimako ga kula da addini.
Sannan kuma sallah ba ta wuce su a jam’i kuma ga yawan nafila da zikiri.
Ashe gidan da mutanen suke zaune, ba a sani ba sun zo da wasu katti wandanda cikin dare mutanen suna ta haka rami a cikin dakin, rami mai zurfin gaske kamar rijiya, sannu a hankali haka har suka doshi inda masallacin annabi yake.
Da daddare sai su kwashe kasar da suka yi hakan, su tafi da ita zuwa can bayan garin Madina su zubar.
Sai da mutanen nan suka yi nisa da ramin nan babu wanda ya sani, burinsu shi ne idan suka kai masallacin Madina inda kabarin Ma’aiki ya ke su huda su shiga.
Sai dai kawai a wayi gari a ga babu kabarin Sayyidina Rasulullahi.
Daya daga cikin manyan sarakuna wancan lokaci sai ya yi mafarki da Manzon Allah, inda ya umarce da ya je Madina domin ana can ana shirya wata makarkashiya a gare shi sallalahu alaihi wasallama, don haka ya je ya yi maganinsu.
Gari na waye wa sai sarki ya tara malaman kasar ya kuma fada musu mafarkin da ya yi.
Malamai suka ba shi shawarar lallai ya je ya ga abin da ke faruwa.
Don haka sai sarkin ya yi shirin yaki ya nufi garin Madina da sojoji sama da 100,000 da kuma manya-manyan makaman yaki na zamanin.
Da isa Madina sai mutane gari suka tambaye shi ko lafiya, shi kuma ya ce ya zo ne ziyara, zai yi sallah ce sannan ya juya.
Yana fada musu sai ya sa aka soma binciken abin da ke faruwa a garin a hankali.
Sarkin ya tambayi wasu manyan garin ko akwai wasu baki a garin da suka sauka, sai suka ba shi amsar cewa da akwai wasu baki da su ka zo garin, amma kuma mutanen kirki ne, suka ba shi labrin irin abubuwan alherin da suke yi da kuma halayensu na gari.
Sai ya ce babu komai watakila dadin barci ne ya sa ya ga abin da ya gani, sai ya juya da rundunarsa ya koma gida.
Sarkin ya kama hanyar gida bai yi nisa da barin Madina ba, sai ya sake wani mafarkin da Manzon Allah kan wannan batun.
Don haka sai sarkin ya juya koma garin ya ce bai yarda da kowa a garin ba.
Sai ya yi umarni da yin bincike gida-gida da nufin gano bakin zaren.
An fara bincike gida-gida, babu tsallakewa, babu babba kuma babu yaro.
Da bincike ya yi nisa sai mutanen garin da kansu suka rika shakku da kalubalantar gidan mutanen nan baki masu aikin alheri, suna mai kare su da cewa bai kamata a shiga gidansu da bincike ba. Sarki ya ki.
Sarki ya bayar da umarnin sai an bincika kamar yadda a aka yi a gidan kowa daki-daki lungu-lungu, kusfa-kusfa har da karkashin gado da kasan kowace tabarma duk a duba.
Hakan kuwa aka yi. Cikin dakin wani daga cikinsu ana daga wani gado sai aka ga rami zurururu, ana shiga ana bin rami sai aka ga ya doshi inda Annabi yake sallalahu alaihi wasallama.
Sai aka soma tuhumar su yadda aka haihu a ragaya.
Da suka sha matsa sai suka yi bayanin abin da ya kawo su da kuma aikin da suke yi.
Ashe kattin nan da ke kwasar kasar da ake haka ramin a bayan Madina suke kwana sai dare ya yi suke zuwa su yi ta kwasar kasar da aka yashe, sannan sai su kai can wajen gari su zubar.
Sarkin nan ya sa aka kama su gaba dayansu aka kashe su.
Gudun kar wani ya sake irin wannan yunkuri a gaba, sai sarkin ya sa aka yi rami dogo adakin Nana Aisha, aka kuma yi katanga mai tsawo aka kewaye kabarin, sai kuma ya sa aka narka dalma da kwalta da bakin karfe.
Idan aka narka kwalta sai a zuba karfe sai kuma a sa dalma, haka aka cike wannan fadin ramin gaba daya aka cike shi ta inda idan ka tasam ma kabarin Manzo Allah ba ka da kayan aiki da kuma fasahar da za ka fasa wannan shingen da za ka kai ga inda fiyayen halitta yake a kwance.
Kamar yadda malaman tarihi suka bayyana, sau biyu ana kai irin wannan yunkurin na kai wa ga inda Sayyidina Rasulullahi ya ke kwance da nufin dauke shi daga wannan wurin.
Wannan bayani na tarihi ya fito ne daga bakin Shehun Malami, Ibrahim Daurawa a wata tambaya da aka yi masa.