Legas ne birni na hudu mafi rashin dadin zama a duniya – Rahoto

0
211
Traffic in market street. Lagos, Nigeria, West Africa

Rahoton binciken birane mafiya dadin zama a duniya (EIU) na 2023 ya bayyana birnin Legas na Najeriya a matsayin birni na hudu mafi rashin dadin zama a duk fadin duniya.

Rahoton dai ya duba birane 173 na duniya, sannan ya yi amfani da hanyoyin bincike iri-iri ya duba fannonin zaman lafiya da kiwon lafiya da al’adu da muhalli da ilimi da kuma abubuwan more rayuwa.

A cewar rahoton, biranen da kawai Legas ya fi dadin zama a duniya su ne Algiers, babban birnin Algeria da Tripoli babban birnin Libya da kuma Damascus, babban birnin Siriya mai fama da rikici.

A bana dai birnin ya ci gaba zuwa mataki na hudu ne sabanin mataki na biyu da yake a bara, sakamakon ingantuwar da aka samu a fannin kiwon lafiya, kodayake rahoton ya e har yanzu akwai matsalar rashawa da ta yi katutu a birnin.

A shekara ta 2022 dai, Legas ne birni na biyu mafi rashin dadin zaman a duk afadin duniya, bayan ya rike matsayin na shekaru biyu a jere, inda ya fi birnin Damascus kawai dadi.

Sai dai rahoton ya ce biranen Vienna, babban birnin Austria da Copenhagen babban birnin Denmark sun ci gaba da rike kambunsu a matsayin na daya da na biyu a cikin birane mafiya dadin zama a duniya.

Kazalika, biranen Melbourne da Sydney na kasar Australia da kuma Vancouver a Kanada su ne suka zo a mataki na uku da na hudu da kuma na biyar a bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here