Gidauniyar Bill Gate za ta kashe Dala biliyan 7 kan harkar lafiya a Najeriya

0
126

Gidauniyar Bill da Milinda Gates ta sanar da cewar za ta zuba Dala biliyan 7 a cikin shekaru 4 masu zuwa domin gudanar da ayyukan inganta harkokin kula da lafiyar jama’a a Najeriya da wasu kasashen Afirka. 

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya bayyana haka a sanarwar ganawar da suka yi da Bill Gates da Aliko Dangote lokacin da suka gudanar da wani taro da ya kunshi gwamnonin jihohi a birnin Abuja. 

Shettima ya ce sun fahimci cewar cutar polio na daya daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar harkokin kula da lafiya a matakin farko, saboda haka wannan tallafi zai taimaka wajen sayen magungunan rigakafi da kuma samar da yanayin da za a rika sarrafa wasu daga cikinsu a cikin gida. 

Mataimakin shugaban kasar wanda ya amince da irin barazanar da kasar ke fuskanta ta bangaren yaki da cutar polio, ya bayyana cewar an samu gagarumar ci gaba a bangaren bai wa yara rigakafi daga kashi 33 a shekarar 2016 zuwa kashi 57 a shekarar 2021, yayin da aka yi nasarar rage kaifin cutar da kashi 84 a shekaru biyu da suka gabata, abin da ya nuna cewar wadanda suka kamu da cutar bara ba su kai 200. 

Shettima wanda ya jinjina wa gwamnonin jihohi saboda rawar da suka taka wajen dakile cutar polio nau’in wanda ke bijirewa magani, ya ce yanzu haka an fadada jihohin da ake yaki da cutar daga 12 zuwa 21 a cikin shekaru. 

Bill Gates da Aliko Dangote sun sake jaddada aniyarsu ta ci gaba da bada gudumawa wajen kawar da polio baki daya daga Najeriya ta hanyar aiki tare da gwamnonin jihohi da kuma gwamnatin tarayya. 

Sanarwar da Daraktan Yada Labaran Fadar Mataimakin Shugaban Najeriya, Olusola Abiola ya gabatar, ta ce shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Alhaji Abdulrahman Abdulrazaq wanda ya yaba da rawar da wadannan attajirai ke takawa wajen kula da lafiyar jama’a, ya kuma jinjina musu akan taimakon da suke bayarwa a bangarori irin na kula da lafiya da ilimi da noma da kuma ci gaban al’umma. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here