Dandazon Musulmai sun taru a Makkah, birni mafi tsarki a tarihin Musulunci, don gudanar da aikin Hajjin da ake sa ran zai zama mafi girma a shekarun baya-bayan nan, inda ake tsammanin fiye da mutum miliyan biyu za su sauke farali.
Ranar Juma’a mahajjata sanye da fararen tufafi da takalman sandal sun taru a birnin mai tarihi, wanda yanzu aka yi wa gine-ginen otel-otel na alfarma da shaguna, bayan sun isa kasar a jirage da motoci da sauran hanyoyi.
Jami’ai sun ce aikin Hajjin bana zai iya kafa tarihi a matsayin wanda za a fi halartarsa.
“A yayin da ake dab da soma aikin Hajji, kasar Saudiyya ta shirya tsaf… domin karbar bakuncin taro mafi girma a tarihin Musulunci,” a cewar Ministan Aikin Hajji da Umrah Tawfiq al Rabiah a wani bidiyo da ma’aikatarsa ta wallafa a wannan makon.
Aikin Hajji ya kunshi yin dawafi da yin salloli a Dutsen Arfat da “jifan Shaidan” da sauransu.
Fiye da mutum miliyan biyu daga kasashe sama da 160 ne za su halarci Hajjin bana, a cewar Rabiah, an samu karin mutum 926,000 daga adadin bara lokacin da aka takaita yawan mahajjata zuwa miliyan daya bayan barkewar cutar korona.
Kusan mahajjata miliyan 1.5 daga kasashen waje tuni suka isa kasar zuwa ranar Laraba, a cewar hukumomin Saudiyya.
A 2019, kusan mutum miliyan 2.5 ne suka gudanar da aikin Hajji. A 2020, mutum 10,000 kacal aka bari su halarci Hajji a yayin da korona ke ganiyarta, amma an bar kusan mutum 59,000 sun yi Hajji shekara daya bayan haka.
Aikin Hajji yana cikin shika-shikan Musulunci kuma wajibi ne kowane Musulmi da ya samu iko ya gudanar da shi akalla sau daya.
Mahajjata daga fadin duniya sun yi ta isa filin jirgin saman Jeddah, inda aka rika daukarsu a motoci domin kai su makwancinsu.
Hukumomi sun ce an ware motocin bas-bas kusan 24,000 da jiragen kasa 17 masu iya daukar mutum 72,000 kowace awa daya domin daukar mahajjata.
Akwai ma’aikatan kiwon lafiya fiye da 32,000 da ke taimaka wa jama’a musamman masu fuskantar matsala sakamakon yanayin tsananin zafin rana a Saudiyya.