Alhazai sun koka kan rashin ishasshen gurin kwana a Mina

0
129
Alhazan Najeriya
Alhazan Najeriya

Tukari sun yi sojan gona a matsayin alhazai tare da mamaye masaukan alhazai a sansanin Mina da ke kasar Saudiyya, lamarin da ya janyo alhazan suka rasa tudun dafawa.

Tun da farko, tukarin sun yi amfani da damar rashin sanin juna tsakanin alhazan, yawansu da kuma zamansu a masaukai daban-daban a Makkah da Madina inda alhaji ba zai iya sanin ko makwabcinsa alhaji ne ko a’a.

An gano cewa sai da jami’an hukumomin alhazai na jihohi suka rika bi shemomi suna fitar da tukari daga ciki tare da maye gurbinsu da alhazan.

A wata shema ta alhazai mata daga Jihar Kano, an fitar da akalla tukari 10 wadanda suke sanye da fararen kaya kamar alhazan, tare da yin magana cikin harshen Hausa.

An gano su ne ta hanyar neman kowacce hajiya ta fito da katin shaidarta, wanda tukarin ba su da ita.

Wakiliyarmu wacce ta zama ganau, ta shaida mana cewa wasu tukarin har sun yi shimfida suna hutawa bayan sun gama karin kumallo da abincin da aka tanada domin alhazan, kafin dubunsu ta cika.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here