Ƙasashen Musulmi na taro a Saudiyya don ɗaukar mataki kan ƙona Al’kur’ani a Sweden

0
181

Kungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya OIC na gudanar da wani taron gaggawa a birnin Jeddah na ƙasar Saudiya domin nazarin matakin bai ɗaya da za a ɗauka kan ƙona Al’qur’ani mai girma da aka yi a ƙasar Sweden a ranar Laraba.

Tattaunawar wadda Saudiyya ta shirya za ta nazarci matakan da suka dace a ɗauka kan abin da ƙungiyar ta kira ”abin Allah wadai” da aka aikata.

Tuni dai ƙungiyar ta yi aAllah wadai kan abin da matashin ɗan asalin ƙasar Iraki da ke gudun hijira a Sweden ya aikata a wajen babban masallacin Stockholm babban birnin ƙasar Sweden ranar Idin Babbar Sallah.

Akasarin ƙasashen musulmi sun gayyaci jakadunsu da ke Sweden domin nuna ɓacin ransu da kuma aike wa da saƙon Allah wadai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here