Abin da ya sa jami’o’in Nijeriya ba sa kan gaba a jerin manyan makarantun Afirka

0
144

Da zarar an ambaci sunan Nijeriya a wasu kasashen duniya, to abu na farko da ke zuwa zukatan mutane shi ne, “Giwar Afirka ko kasa mafi yawan jama’a a nahiyar ko kasar bakaken-fata mafi yawan jama’a a duniya,” da dai sauran su.

Nijeriya ta yi fice a fannoni daban-daban kamar kwallon kafa, inda fitattun ‘yan wasan Kungiyar Super Eagles suka kara samo mata suna a duniya.

Sannan arzikin danyen man fetur da take da shi wani abu ne da ya sa ta yi fice.

Amma sai dai wani abin mamaki shi ne yadda kasar ke samun kanta a baya idan aka zo batun wasu fannoni a nahiyar, irin su ilimi da lafiya.

A karshen watan Yunin da ya wuce, Kungiyar Times Higher Education mai fafutukar ganin makarantun duniya sun yi zarra, ta wallafa jerin jami’o’in da suka fi kwarewa a bincike da koyarwa a nahiyar Afrika.

Rahoton ya yi nazari ne kan jami’a 88 a kasashe 20 na nahiyar.

Jami’ar Witwatersrand ta Afirka ta Kudu ce ta zo ta farko a jarin. Hoto:  University of the Witwatersrand 

Kungiyar na fitar da jerin ne saboda kokarin magance matsalolin da fannin ilimin gaba da sakandare ke fuskanta a nahiyar da ke da mutum fiye da biliyan daya.

Sai dai abin mamaki, babu wata jami’ar Nijeriya da ta shiga jerin biyar din farko, daga cikin kusan 100 da aka fitar.

Wasu jami’o’in kasar Afirka ta Kudu ne suka yi na daya da na biyu da kuma na hudu, yayin da wata jami’a ta kasar Tanzaniya ta yi ta uku, sai wata jami’a a Uganda da ta yi ta biyar.

Jami’ar da ta yi ta bakwai ta Nijeriya ce mai zaman kanta mai suna Covenant University, wadda ba wata fitacciya ba ce sosai idan aka kwatanta da manyan jami’o’i mallakin gwamnatin kasar.

Yawancin manya kuma fitattun jami’o’in Nijeriya irin su Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria da Jamai’ar Bayero ta Kano da Jami’ar Obafemi da ta Ibadan duk suna can kasa a jerin.

Rashin kai labari

Me ya sa fitattun jami’oin Nijeriya ba su fiye zama a kan gaba ba a irin wannan lamari, ta yadda har jami’o’i masu zaman kansu ke fin na gwamnati tagomashi?

Wannan ita ce tambayar da yawancin mutane suke yi, musamman ganin cewa ana magana ne a kan jami’o’in Afirka ba wai na duniya baki daya ba.

Jami’ar Covenant mai zaman kanta a Nijeriya ita kadai ce ta samu cikin na goman farko a jerin daga cikin jami’o’in kasar. Hoto: Covenant University

Dokta Aliyu Tilde, kwarrare ne kan fannin ilimi a Nijeriya, ya shaida wa TRT Afrika cewa duk da cewa yawancin kungiyoyin da ke fitar da irin wadannan alkaluma akwai ka’idojin da suke la’akari da su, a bayyane yake cewa jami’o’in Nijeriya, musamman na gwamnati, na cikin mawuyacin yanayi da ba za a yi mamakin ganinsu a kasan jerin makarantun da suka fi kyau ba a Afirka.

“Irin matsalolin da makarantun firamare da na sakandare ke fama da su a Nijeriya su ne a yanzu suke shafar jami’o’i ta yadda har makarantun kudi suke fin na gwamnati tagomashi,” in ji masanin.

Ya ci gaba da cewa “cunkoson dalibai irin wanda ake samu a makarantun firamare da sakandare, su ma yanzu jami’oin haka suke.

“Alal misali, lokacin da muka gama jami’a shekara 40 da suka wuce, mu shida kadai muka kammala a kwas din da na yi a Jami’ar Ahmadu Bello.

“Amma yau a wannan kwas din za a iske daruruwan mutane kuma ba a kara yawan dakuna da malamai da dakunan karatu da na bincike da ofisoshi ba, amma kuma an tuttulo dalibai da yawa.”

Manyan Jami’o’i irin Jami’ar Bayero ta Kano ba su kai labari ba a na gaba-gaba a jerin. Hoto/Bayero University Kano

Kazalika Dokta Tilde, wanda tsohon kwamishinan ilimi ne a Jihar Bauchi, ya ce yawan al’ummar Nijeriya da yadda ake banzatar da ilimin jami’ar da cin hanci da rashawa da ya baibaye fannin, na daga cikin manyan matsalolin da suke damun jami’o’in kasar.

Ya kuma koka kan yadda a yanzu harkar rashawa ta samu gindin zama a cikin harkokin jami’o’in gwamnati a Nijeriya ta yadda ”kowa kallon maslahar aljihunsa yake yi.”

Ita dai wannan kungiya da ta fitar da wannan jeri na makarantu ta ce ta yi la’akari ne da ma’auni biyar wajen yin hakan. Ma’aunan su ne:

  • Yawan kudaden da kowace jami’a ke da su don tafiyar da al’amuranta
  • Yadda kowace jami’a take kokarin samar da daidaito a tafiyar da harkokin dalibai
  • Ingantaccen tsarin koyarwa da kuma kwarewa wajen koyarwar
  • Irin matakan da kowace jami’a take dauka wajen horar da dalibanta da ba su damarmaki na samun kwarewa
  • Tasirin da kowace makaranta take da shi a kasarta da nahiyar Afirka.

To ko zamowar fitattun jami’oin Nijeriya a kasa-kasa a wannan jeri na nufin a yanzu kwalayen digirin da ake samu a can ba su da wani tasiri kenan?

Dokta Tilde ya ce hakan ba zai shafi darajar kwalayen karatun jami’o’in ba, “wannan ya danganci ka’idojin da aka sa ne wajen auna jami’o’in, kuma kowace kungiya na da ka’idojin da take bi, don babu wata jami’a a duniya da za a ce 100 bisa 100 ta cika dukkan ma’aunan da ake bukata.”

Sai dai masanin ya jinjina yadda kasancewar jami’o’in gwamnatin Nijeriya a kasan ma’aunai irin haka a Afirka ka iya taba kimar kasar a idon duniya.

“A da lokacin da muka gama jami’a da ka je Ingila a take za a dauke ka ci gaba da karatu babu wata damuwa, amma a yanzu sai sun sake jarraba mutum.

“Kenan akwai alamar tambaya kan karkon kwalayen da hukumomin jarrabawa da kuma jami’o’inmu suke bayarwa.”

Ina mafita?

Komawa ga ainihin turbar da ake ba da ilimi a kai yadda ya kamata ita ce babbar mafita ga wannan matsala, in ji Dokta Tilde.

Jami’ar Ahmadu University ta Zaria ma ita ce ta 46. Hoto: ABU

“Idan ana so a ga sauyi don jami’o’in Nijeriya su yi wa sauran na kasashen Afirka fintinkau, dole sai an tashi tsaye an gudanar da abubuwa a yadda suka dace.

“A tabbatar da daukar dalibai daidai adadin da jami’a za ta iya lura da su ta ba su karatu mai inganci, sannan a samar da isassun kayan aiki da duk abubuwan da malamai da dalibai ke bukata don aiwatar da aikinsu yadda ya dace.”

Ya kuma ce watakila samuwar makarantun kudi na jami’a su share hawaye kan wasu matsalolin domin “gyara abu a gwamnati yana da wahala.”

Kazalika yana ganin a wannan mataki da ake na ci gaba a duniya a yanzu “ba sai Nijeriya ta je wani waje ta koyo yadda za ta gyara matsalolin fannin ilimi ba, shegantaka ce kawai da kowa ya saka a ransa ta ba a son kawo gyara.

“Kowane malami a jami’a da shugabannin jami’o’i da sauran hukumomi kowa ya san matakin kawo gyara a fannin nan.”

Baya ga haka, Dokta Tilde yana ganin rashin yin nazari da bincike sosai a jami’o’in Nijeriya na daga cikin abubuwan da ke sanya su a kasa.

“A duk lokacin da aka auna jami’o’in Nijeriya bisa ga ma’aunin bincike to gaskiya za a samu babu abin kirki don hankula sun fi karkata kan me za a samu,” a cewar masanin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here