Gwamnatin Nijeriya za ta soma aiki da na’ura don karbar haraji daga ‘yan tireda

0
106

Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta soma aiki da kungiyar kananan ‘yan kasuwa domin karbar haraji daga miliyoyin ‘yan tireda a yunkurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kara fadada tattara haraji.

A wata sanarwa da Hukumar Tattara Haraji ta Nijeriya, FIRS, ta fitar a ranar Litinin ta ce tana kokarin hadin gwiwa da kungiyar kananan ‘yan kasuwa ta MATAN domin karbar haraji daga mambobinta.

Ta ce za ta mayar da hankali musamman wajen amfani da na’urori wurin karbar harajin.

Nijeriya na daga cikin kasashen da ake da karancin karbar haraji a duniya inda ake karbar kashi 10.8 cikin 100 kamar yadda FIRS ta bayyana.

Kashi 47 cikin 100 na kasafin kudin 2023 zai fito daga haraji da sauran bangarori na rance.

Kasar, wadda ta fi kowace karfin tattalin arziki a fadin Afirka, ta dauki gagaruman matakai wadanda suka hada da cire tallafin man fetur da cire takunkumi kan hada-hadar kudaden waje, a kokarin gwamnatin ta Tinubu na habaka tattalin arzikin kasar.

Bibiyar kudin haraji

An bayyana cewa wannan hadin gwiwar zai taimaka wurin dakile ayyukan ‘yan tasha da wadanda suke gaban kansu wajen karbar haraji ba bisa ka’ida ba a kasuwanni.

Sabon tsarin tattara harajin, wanda ake kira ‘VAT Direct Initiative’, tsari ne wanda za a yi amfani da manhajar zamani wurin bibiyar harajin da kananan ‘yan kasuwa suke biya da kuma saka kudin cikin asusun harajin kasa.

Hukumar tattara harajin ta bayyana cewa mambobin MATAN za su samu katin shaida, da kuma lambar biyan haraji wadda za ta taimaka wurin bibiyar kudin da suke biya.

Abubuwan more rayuwa

Ana sa ran kungiyar ta kananan ‘yan kasuwa za ta rinka wayar da kan mambobinta kan tsarin, kamar yadda sanarwar gwamnatin kasar ta bayyana.

Wannan ne karo na farko da Nijeriya ke kaddamar da irin wannan tsarin ta hanyar amfani da kimiyya wurin karbar wannan haraji. Babu tabbaci kan adadin kudin da gwamnatin ta Nijeriya ke son samarwa daga wannan tsarin.

Tsawon lokaci, ‘yan Nijeriya sun dade suna kokawa kan cewa gwamnatin kasar ba ta cika samar musu da ababen more rayuwa ba duk da harajin da gwamnatin kasar take karba.

Sai dai gwamnatin kasar ta ce a karkashin wannan sabon tsarin, harajin zai samar da “karin kudi domin samar da ababen more rayuwa domin amfanar jama’ar kasa”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here