An ci tarar Neymar Dala miliyan 3.5 kan zargin karya dokar muhalli

0
142

Hukumomin Brazil a ranar Litinin sun bayyana cewa an ci tarar shahararren dan kwallon kafar nan na kasar Neymar dala miliyan 3.33 kan zarginsa da laifin saba ka’idar muhalli.

Hukumomin kasar sun ce dan wasan gaban na Paris Saint-Germain ya saba ka’idar a lokacin da ya gina katafaren gidansa da ke kudu maso gabashin Brazil.

Hukumomin sun ce a yayin da ake ginin, an rinka amfani da ruwa da duwatsu da kasa ba bisa ka’ida ba.

Sai dai mai magana da yawun dan wasan mai shekara 31 ya ki yarda ya yi karin bayani kan wannan lamari.

Gidan dan wasan yana gundumar Mangaratiba da ke kudancin Jihar Rio de Janeiro ta Brazil.

Hukumomin Mangaratiba a sanarwar da suka fitar ranar Litinin sun bayyana cewa an saba ka’idar muhalli a yayin ginin gidan dan wasan wanda aka gina tafki a ciki.

Baya ga tarar da za a yi wa dan wasan, ofishin antoni janar na jihar da ‘yan sandan jihar da hukumar kare muhalli da sauran hukumomi da ke da ruwa da tsaki a lamarin za su gudanar da bincike a kai.4

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here