‘Yadda na rasa hannuna yayin da nake kare al’ummata’

0
178

“Ban yi nadaman rasa hannuna ɗaya ba saboda haka Allah ya ƙaddara min ranar, kuma a yau al’ummata na karrama ni.”

“Wani abun da ya yi mun zafi shi ne matata ta mutu watanni kaɗan bayan na rasa hannuna. Tunanin abin da ya faru da ni ya yi matukar damun ta.”

Haka ne Sani Inusa wanda aka fi sani da suna Ofisa Babangida, da ke yankin Tudun Fulani a jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ya fara yi wa BBC bayanin yadda ya rasa hannu ɗaya kuma ya kusa rasa ransa a hannun wasu ‘yan fashi da makami.

Al’ummar da ke zaune a Tudun Fulani, sun dauki Babangida a matsayin babban Jarumi ganin yadda ya yi iyakar ƙoƙarinsa wurin tabbatar da cewa ɓata-garin da ke neman tayar da husuma a yankin ba su yi nasara ba.

“Babu ofishin ‘yan sanda ko ɗaya a daukacin yankinmu, abin da ya sa na shiga kungiyar ‘yan banga, shekaru biyar da suka wuce. Saboda in samu damar bayar da tawa gudumawar wurin kiyaye al’umma daga ɓata-gari.”

Muna da matasa da dama da ke yin fataucin miyagun kwayoyi, da cin zarafin mutane da kuma sata, kuma idan ka yi la’akari da rashin ‘yan sanda, ko wata hukumar tsaro a yankinmu, ba ƙaramar matsala ba ce.” A cewarsa.

“Ba mu da asibiti kuma babu wutar lantarki a yankin. A gaskiya a lokacin damina, da yawa daga cikin mutane sun guje wa yankin saboda hanyar ba ta da kyau ko da kuwa a ƙafa ne.”

Mahaifin ƴaƴa huɗun ya ce abin da ya fi ci masa tuwo a ƙwarya shi ne duk da cewa kuri’un da aka kaɗa na bai wa ‘yan siyasa mulki ba su sa wasu abubuwan more rayuwa a yankin ba.

‘Yadda na rasa hannu na’

...
Bayanan hoto,Sani Inusa ya rasa hannu daya yayin da yake kokarin hana miyagun mutane tasiri a al’ummarsu

Babangida ya ce a ranar 18 ga watan Janairun 2023, yana gidansa yana kokarin kammala wani aiki sai ya samu kiran waya na gaggawa na neman taimako.

“Ina ɗinka wasu kujeru ne saboda aikin da nake yi na ƴan-banga ba biyan mu ake yi ba, taimakon al’umma ne.”

Da misalin karfe 3:00 na safe sai aka kira ni cewa wasu ‘yan fashi da makami sun shiga gidan makwabtana, don haka na yi maza na fita.”

Sai dai Babangida bai bai san cewa ‘yan fashin sun fi su yawa ba, da yake daga shi sai abokin aikinsa ne suka yi yunkurin kai agajin.

“Abin takaici shi ne mu biyu ne kawai muka fito kuma ‘yan fashin sun kai 50 sai suka fara amfani da makaman da ke hannunsu wurin kai mana hari.

Sun sassare ni a hannu da adduna da kuma wukake saboda a lokacin da suka afka mana na yi kokarin tare dukan da hannuna.

...
Bayanan hoto,Babangida ya samu raunuka da dama a bayansa sakamakon harin

Rasuwar matarsa

Abokin aikina shi ma an sassare shi sama da sau 50. A nan suka bar mu jina-jina suna tunanin cewa mun mutu.”

Babangida ya samu damar rarrafawa ya isa wani wuri inda mutane suka taimaka suka kai shi asibiti.

“Na yi tafiya mai nisa kafin wasu mutane suka gan ni suka dauke ni zuwa asibitin Murtala.”

“A nan ne likitoci suka ce hannuna ya lalace kuma dole sai an yanke kuma duk da haka ɗayan hannun nawa ma ya kakkarye kuma ba zan iya amfani da shi da kyau ba.”

...
Bayanan hoto,Babangida ya ce matarsa ta rasu jim kadan bayan lamarin ya faru

Babangida ya ce harin da aka kai masa ya matukar girgiza matarsa .

“Kodayaushe takan yi tunanin abin da ya faru saboda lokacin da na fita, ba mu dade da gama hira da ita ba kafin ta yi barci” A cewarsa.

Kwanaki kadan bayan faruwar lamarin sai ta fadi, sai kuma ba ta dawo daga asibiti da rai ba.

Babangida ya ce yana waje sai daya daga cikin yaransa ya ruga ya gaya masa cewa mahaifiyarsu ta fadi daga gadonta.

“Mun kai ta asibiti inda muka shafe kwanaki a nan kafin ta mutu.”

Ba zan daina yaƙi da miyagun mutane ba

...
Bayanan hoto,Babangida ya samu karaya a daya hannun

Babangida ya ce duk da halin da yake ciki, yana farin ciki idan ya tuna wasu abubuwan da hannayensa biyu suka cimma kafin faruwar lamarin.

“Lokuta da yawa na faranta min rai idan na tuna saboda duk da abin da ya faru a ranar 18 ga watan Janairu, ba karamin takura wa miyagun mutane muke yi a Tudun Fulani ba.”

”Ko cikin kwanakin nan mun kama dillalan miyagun kwayoyi da ’yan fashi da makami, inda muka kai su Bachirawa ko ofishin ’yan sanda na Gwale.” A cewarsa.

Duk da cewa hannu daya ne da shi, kuma daya hannun ba shi da isasshen lafiya, ko wace rana Babangida na zuwa ofishin ‘yan banga don bayar da tasa gudumawar wurin tabbatar da tsaro a yankin.

”Kullum sai na je wurin saboda a nan ne muke tattauna harkar tsaron yankinmu.”

”Ina faɗa muku ko cikin kwanakin nan, na bayar da gudummawa yayin da muka kama wasu ’yan bindiga da suka ziyarci yankin suka sace kananan yara”.

”Ba zan yi ƙasa a gwiwa ba saboda abin da zan iya yi domin taimaka wa mutanena da al’ummata ke nan.” A cewarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here