Tottenham ta yi wa Harry Kane, gwaggwaban tayi inda za ta kara masa albashi sosai da ya fi wanda yake karba yanzu a duk mako na fam dubu 200, domin ya ci gaba da zama a ta Landan. (Guardian)
To amma kuma kociyan Bayern Munich Thomas Tuchel ya yi takakka takanas ya je har gidan kyaftin din na Ingila ya gana da shi domin shawo kan Kane din ya je koma kungiyar ta Jamus. (Bild daga Mail)
AC Milan ta sake gabatar da wani tayin da ya fi wanda ta yi a da na neman Chelsea ta sayar mata da Christian Pulisic dan Amurka a kan dala miliyan 24. (Mail)
Manchester United na shirin gabatar da tayin da ya kai fam miliyan 39 a kan golan Inter Milan, Andre Onana, dan Kamaru. (Fabrizio Romano)
Arsenal ta yarda ta sayi matashin dan bayan Ajax, Jurrien Timber dan Netherlands mai shekara 22, a kan fam miliyan 8 da rabi (Standard)
Da wannan, cefanen da Gunners din za ta yi a bazara zai kai kusan na fam miliyan 200, bayan cinikin Timber da Declan Rice. (Telegraph)
Newcastle na kan gaba wajen zawarcin dan wasan tsakiya na Leicester City Harvey Barnes, dan Ingila, wanda Aston Villa da Tottenham su ma suke so. (Guardian)
Chelsea na shirin gabatar da tayin da ya kai na fam miliyan 85 a kan matashin dan wasan Brighton Moises Caicedo dan Ecuador mai shekara 21. (Diego Arcos, daga Football.London)
Haka kuma Blues din na sha’awar sayen dan wasan tsakiya na Southampton Romeo Lavia, dan Belgium mai shekara 19. (Sky Sports)
Sabon dan wasan da Manchester United ta saya Mason Mount, mai shekara 24, ya yi watsi da tayin albashin fam dubu 200 a mako da Chelsea ta yi masa domin hana shi tafiya daga Stamford Bridge a watan Fabarairu. (Athletic)
Aston Villa da Everton na cikin kungiyoyin Premier da suke son sayen matashin dan gaban Leeds United Wilfried Gnonto, dan Italiya mai shekara 19. (Football Insider)
Har yanzu Liverpool na son matashin dan bayan da Chelsea ba ta son rabuwa da shi Levi Colwill, dan Ingila mai shekara 20. (Football.London)
Kociyan DC United Wayne Rooney ya ce yana son ya ci gaba da rike dan wasan tsakiya da ya aro daga Nottingham Forest Lewis O’Brien, wanda Sheffield United ita ma ke son saye. (Mirror)