Mai Facebook ya yi wa Twitter kishiya

0
140

Katafaren kamfanin fasaha na Meta wanda ya mallaki shafin Facebook da Instagram, ya kaddamar da manhajar sabon shafinsa na sada zumunta da muhawara, mai suna Threads, da galibi ake kallo a matsayin kishiya ga Twitter.

Shafin na Threads, yana dauke da abubuwa kamar yadda Twitter yake kuma wanda yake da shafin Instagram zai iya samunsa ta wannan shafin cikin sauki.

‘Yan sa’o’i da kaddamar da shi shafin har ya fara samun miliyoyin jama’a.

Ba ma ga kwararru ba da suka kalli kaddamar da wannan sabon shafi ko manhaja ta Threads a matsayin kishiya ga Twitter mallakar Elon Musk, Mark Zuckerberg mai katafaren kamfanin Meta da ya mallaki Facebook da Istagram ya furta da kansa cewa Threads wanda ya kunshi abubuwa da ke kusan irin na Twitter zai kasance kishiya da nufin wuce Twitter.

Bugu da kari kwararru sun ce Threads zai iya janye masu amfani da Twitter, wadanda ba su ji dadin wasu sauye-sauye da aka bullo da su a baya-bayan nan ba a manhajar ta Twitter.

Duk da cewa zuwa yanzu ba a kaddamar da wannan sabon shafi na sada zumunta da muhawara ba a yankin Tarayyar Turai ba, to amma Mista Zuckerberg ya ce a cikin sa’a hudu da kaddamar da shi har ya samu masu amfani da shi sama da miliyan biyar.

Kuma tun da farko ya nuna cewa yadda za su saukaka amafani da shafin ya kasance abokin mu’amullar mabiya hakan zai kasance abin da zai kai shi ga gagarumar nasara.

To amma mai manhajar Twitter, Elon Musk ya mayar da martani da cewa ,

gara a ce baki a Twitter sun farmake ka da a ce kana yake a kan Instagram, wanda ya gaza.

Shi kuwa Zuckerberg da aka tambaye shi ko yana ganin sabon shafin nasa zai kai zarta Twitter”, sai ya ce zai dauki lokaci , amma yana ganin zai kasance shafin da ke da mutane miliyan dubu da doriya.

Ya kara da cewa Twitter ya samu wannan dama amma bai yi amfani da ita ba. Amma ya ce su suna fatan za su yi.

Sai dai abokan gogayya sun yi suka a kan yawan bayanan da manhajar za ta rika amfani da su na mabiya.

Wadanda sun hada da batun lafiya da na kudi da kuma na bayanan mai shiga shafin , in ji rumbum Apple Store.

A yanzu dai ana iya sauke wannan manhaja ta sabon shafin na sada zumunta da muhawara na Threads, a sama da kasashe 100, ciki har da Birtaniya, amma ban da kasashen Tarayyar Turai.

Kamfanin Meta da ya mallaki wannan sabuwar manhaja ya ce, a yanzu zubin farko ce, wanda hakan ke nufin akwai karin wasu abubuwa da ya shirya sanya wa manhajar domin kara jan hankalin jama’a

Kasancewar shafin nada alaka da Instagram wanda ke da tarin mabiya, wannan zai sa ya samu saukin daukar hankalin tarin miliyoyin mabiya da ke kan Instagram, wadanda tuni wasui ma har sun damfara da sauke shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here