Hukumar MACIN ta bukaci jami’an tsaro su hana Ganduje tserewa daga Najeriya

0
160
Ganduje
Ganduje

Wata kungiya Mai rajin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya mai suna Movement Against Corruption in Nigeria (MACIN) ta yi kira ga ‘yan sandan Kasa da kasa na Interpol da hukumar lura da shige da fice ta Najeriya su sanya idanu ka tsohon gwmanan Kano Abdullahi Umar Ganduje domin kada ya tsere sakamakon bincike da ake masa kan zargin cin hanci.

A yayin wani taron manema labarai da jagoran kungiyar kwamared Kabiru Sa’idu Dakata ya gabatar, ya nemi hukumomin su sanyawa tsohon gwmanan na Kano idanu, domin Shirin fucewa da yake zuwa ketare bayan da hukumar yaki da cin hanci ta jihar ta nemi ya bayyana a gaban ta domin amsa tambayoyi kan wani fai-fan bidiyon da aka ganshi yana karba tare da cusawa Dalar Amurka a aljuhun sa abin da ake zargin na cin hancin kwangiloli ne.

Kwamared Kabiru Sa’idu Dakata ya Shawarci tsohon gwmanan Daya amsa gayyatar hukumar domin gaskiya ta yi halinta, kodai a wanke shi daga zargin ko kuma ya amsa laifin sa.

Kazalika kungiyar ta yi kira ga shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu da kada ya Bada dama a lullube mutanen da ake zargi da cin hanci a gwamnatin sa.

Ana dai zargin tsohon gwmana Ganduje da karbar kudi da aka ce sun tasamna Dala miliyan biyar na cin hanci lokacin yana kan gwamnan jihar.

Tuni dai hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta dawo da aikin binciken, bayan da kwararru suka tabbatar mata da cewar faya-fayan bidiyon na da sahihanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here