A yayin wani gagarumin taro da suka yi a Abuja, Shugabanin Kungiyar kayayyakin da ake nomewa wato NACP, sun nuna damuwar su kan yadda harkar noma ke shan wahala wajen samun tallafi daga bangaren gwamnati.
ABUJA, NIGERIA -A hirarta da Muryar Amurka, shugabar kungiyar Madam Florence Edward ta bayyana cewa, sun fi son Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samu goggagen masanin harkokin noma kuma wanda yake da alaka da manoma domin jagorantar harkar noman kasar yadda ya kamata.
Florence ta ce an kwashi shekaru da dama ana cewa gwamnati tana tallafawa harkar noma amma har yanzu manoma ba su gani a kasa ba.r
Shi kuwa Shugaban Manoman Masara ta Kasa Bello Abubakar Anur ya nuna cewa hanya daya da za a iya farfado da tattalin arzikin kasar ita ce ta inganta harkar noma.
Annur ya ce kungiyar tana son gwamnati ta fahimci cewa, akwai matsaloli da dama da manoma ke fuskanta musamman ma a yanzu da aka janye tallafin man fetur.
A nashi jawabin Shugaban Kungiyar masu fatauci, kiwo da sarrafa naman saniya ta kasa Iliyasu Bulama ya yi tsokaci cewa da dadewa ana magana ne akan Makiyaya da Fulani, amma kuma duk ba a fahimci inda matsalar ta ke ba.
Iliyasu ya ce matsalar tana wajen mai kiwon saniya ne, saboda ba a killace masu wurin da ya kamata su zauna ba. Iliyasu ya kuma cewa yadda noma ya zama wajibi haka kiwo ya zama wajibi, saboda haka yana kira ga Gwamnati da ta yi kokarin magance rashin jituwa da ke wanzuwa tsakanin Makiyaya da Manoma ta hanyar killace su makiyayan saboda a yi maganin yawan matsalolin tsaro da ke tasowa a tsakaninsu.