Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta ƙasa (NCAA) ta dakatar da kamfanin Max Air daga amfani da samfurin jiragen Boeing 737 a Najeriya.
Daraktan NCAA Kyaftin Ibrahim Bello Dambazau ne ya sanar da haka cikin wata wasiƙa da ya aike wa kamfanin.
Kyaftin Dambazau ya ce an dakatar da ayyukan Max Air nan take saboda matsalolin da ake samu tattare da jiragen kamfanin samfurin Boeing B737.
Ya ce matsalolin sun haɗa da lalacewar tayar jirgin Max Air da ya tashi daga Yola zuwa Abuja ranar 7 ga Mayun 2023.
Akwai kuma gurɓatar mai da aka samu a jirgin Max Air da ya haddasa wutar lantarkin jirgin ta ƙi aiki ranar 7 ga Yulin 2023 a tashar jiragen sama ta Yola.
Matsala ta uku ita ce zafin da injin jirgin ya ɗauka a ranar 11 ga Yulin 2023 a tashar jiragen sama ta Malam Aminu Kano, abinda ya sa jirgi ya kasa tashi.
Sai kuma sauka ba shiri da jirgin ya yi a tashar jiragen sama ta Nnamdi Azikiwe dake Abuja sanadiyyar ɗaukar zafin da mazaunin matuƙar jirgin ya yi ranar 11 ga Yulin 2023.
Daraktan na NCAA ya ce hukumar ta kafa kwamitin masu bincike da za su yi tantance ingancin jiragen Max Air.
Ya ƙara da cewa ba za a ƙyale Max Air ya ci gaba da amfani da jiragen Boeing 737 a Najeriya ba har sai bayan kammala binciken.