Babban Hafsan hafsoshin sojojin Najeriya, Manjo Janaral Taoreed Abiodun Lagbaja ya bayyana cewa yin ahuwa ko yafiya ba shi da wani tasiri a yaki da ta’addanci ko shawo kan matsalar tsaro a Najeriya.
Babban Hafsan sojin yace, ‘yan bindiga ba zanen goyo bane, kasancewa yin sulhu ko afuwa ba abinda ya ke tsinanawa sai kara basu damar kara karfi su sake tattaruwa domin shirya sake ci gaba da kaddamar da hare-hare.
Bisa wannan matsayar Janaral Lagbaja ya umarci Babban Hafsa mai kula da kai hare-hare ya tsara yadda za a tunkari matsalar rashin tsaro a jihar zamfara.
Janaral Lagbaja wanda ke magana lokacin da Gwamnan jihar Zamfara Dr. Dauda Lawal Dare ya ziyarce shi domin kai koken irin yadda ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka, ya ce duk wata matsala da ta shafi Zamfara, to zama Illa a jihohin Kaduna, Kebbi, Katsina da Niger.
Bisa wannan dalilin ya ce za a shirya kaddamar da farmakin bai daya lokaci guda tsakanin dakarun runduna ta daya dake Kaduna da kuma mayakan runduna ta takwas da ke Sokoto ta yadda in an afkawa ‘yan bindigan daga Kudu ba za su sami damar tserewa zuwa Arewa ba, ko in an afka masu daga Arewa ba za su samu damar tserewa zuwa Kudu ba.
Babban Hafsan Hafsoshin na Najeriya ya bayyana cewa abubuwa da dama ne suka assasa kalubalen tsaro a jihar Zamfara, kamar rigimar Makiyaya da Manoma, rikicin ‘Kabilanci da matsalar da ke da alaka da hakar ma’adinai, banda haka kuma, dukan bangarorin na rike da makamai.
Ya ce don tunkarar wannan matsala dakarun za su dauki kwakkwaran matakin yiwa tufkar hanci inda ya kara nuna lalle batun sullhu ko afuwa ga ‘yan ta’adda ba zai yi wani tasiri ba.