Amincewar da zaurukan majalisar dokokin tarayya biyu suka yi da kuɗi naira biliyan 70 don tallafa wa kansu na tayar da ƙura a Najeriya.
Wasu ƴan Najeriya a shafin Tuwita sun tuhumi lokacin da aka amince da kuɗin, musamman ganin lamarin ya zo ne sama da wata ɗaya bayan gwamnatin ƙasar ta cire tallafin man fetur.
Cire tallafin man fetur ya haifar da tsadar sufuri da tashin farashin kayan abinci.
Eniola Akinkuotu;
“Akwai wakilci na jam’iyya bakwai a Majalisar Dokokin Tarayya, ciki har da LP da PDP da kuma NNPP. Duk da haka babu ɗaya daga cikin ƴan majalisar da ya ƙi amincewa da batun naira biliyan 70 a wannan lokaci na tsanani. Za ku iya ganin cewa ƴan siyasar Najeriya ba sa faɗa idan aka zo batun kuɗi.”