Tinubu ya sauya shawara kan tallafin dubu 8

1
159

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bada umarnin yin garambawul ga shirinsa na raba N8,000 ga matalauta domin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur.

Kakakin shugaban ƙasa, Dele Alake ya ce shugaban ya sauya shawara kan shirin ne sanadiyyar sukan da yake sha daga  ƴan Najeriya.

Tuni dai Majalisar Dattawa ta sahhalaewa Gwamnatin Tarayya raba N8,000 ga matalauta miliyan 12 tsawon watanni shida.

Sai dai Mr. Alake ya ce bayan da shirin ya sha suka daga ƴan ƙasa, shugaba Tinubu ya umarci jami’ansa su fito da tsarin da zai fi tasiri wurin ragewa al’umma raɗaɗin janye tallafin.

Ya kuma ce kafin akai ga fito da sabon tsarin, shugaba Tinubu ya bada umarnin raba takin zamani ga manoma miliyan 50 a faɗin Najeriya nan take.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here