Tsadar fetur da abinci: Halin taraddudi da ‘yan Nijeriya ke ciki

0
131

‘Yan Nijeriya sun shiga halin taraddudi a wannan makon yayin da farashin man fetur da kayayyakin masarufi suka yi tashin gwauron zabi.

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawan farashin kayan abinci a watan Yunin 2023, ya kai kashi 22.79 a cikin dari idan aka kwatanta da na watan Mayun 2023, da ya kasance da kashi 22.41 a cikin dari.
Wannan na kunshe a cikin rahoton farashin kayan abinci (CPI) na wata-wata da NBS ta fitar a makon nan. A cewar rahoton NBS, karin farashin ya kai kashi 0.38 a cikin dari, inda rahoton ya yi karin hasken cewa idan aka duba mizanin shekara-shekara, za a ga cewa farashin ya karu ne da kashi 4.19 a cikin dari, idan aka kwatanta da wanda aka samu a watan Yunin 2022 da bai wuce kashi 18.60 a cikin dari.
NBS ta ce, an samu karuwar farashin ne a kan kayayyaki kamar su, man girki, burodi, hatsi, dankali, doya, kifi, nama, kwai, kayan lambu da sauransu.

Sauran harkokin da aka samu karin farashin su ne, sufuri, iskar gas, kayan gyaran ababen hawa, kiwon lafiya da bakin mai.
Sai dai ‘Yan Nijeriya ba su gama jimamin tsadar farashin kayan masarufin ba, kwatsam sai ga sanarwar karin farashin litar man fetur daga Naira 539 zuwa naira 617 a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ana kyautata zaton karin farashin man ba zai rasa nasaba da batun da ‘yan kasuwar man suka yi cewa farashin na iya kaiwa Naira 700 kan kowace lita ba a kwanan baya.

LEADERSHIP Hausa ta bibiyi ra’ayoyin wasu ‘Yan Nijeriya a kafafen sadarwa daban-daban domin jin halin da suke ciki inda galibi suka yi bayanin cewa a gaskiya suna jin jiki.

Bashir Bello ya bayyana cewa, “Ga talauci ga yunwa ga tsadar rayuwa ga kuncin rayuwa ga rashin tsaro. Wai ni Allah! Ina ake so talaka ya sa kansa ne? Allah ya kawo mana karshan wannan lamarin a kasar nan.”
Haka zalika, Aliyu Umar ya fadi cewa, “Allah ya kara shiga lamuranmu. Amma duk ranar talaka ya fara bore a Nijeriya mai tare shi sai Allah.”

Shi ma da yake bayyana nashi ra’ayin, Nuhu Mika’il ya bayyana cewa, “Masu mulki ku ji tsoran boren talakawan Nijeriya. Domin duk ranar da talakawan Nijeriya suka yi bore, sai dai masu mulki su yi hijira.”

A nasa ra’ayin kuwa, Muhammad Sani ya bayyana cewa, “Duk wannan ce-ce-ku-ce da ake yi kan tsadar rayuwa ba na kallon hakan mafita, domin tsadar rayuwar tana wa wasu fa’ida saboda burinsu kenan. Allah za mu roka mafita tare da kyautata halayyenmu.”

Da yake bayyana ra’ayinsa, Hamza Unikue Hamza ya bayyana cewa, “Talakawan Nijeriya suna ganin hisabin duniya kam. Allah Ubangiji ya saukaka mana tsadar rayuwa da muke ciki, Amin.”

A lokacin da yake bayyana nasa ra’ayin, wani dan kasuwa, Malam Kabir Garba ya bayyana cewa, “’Yan Arewa dole ne ku bai wa Jagaba uzurin kamar yadda kuka bai wa Muhammadu Buhari, saboda shi gyaran targade dama haka yake zuwa da tsananin zafi.”

Ga dukkan alamu dai mafi yawancin ‘yan Nijeriya ba su ji dadin wannan tashin gwauron zabon da farashin man fetur da kayan masarufi ke ci gaba da yi ba, musamman yadda ake ci gaba da samun matalauta a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here