Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta nanata cewa babu wani shirin kara kudin kiran wayar tarho sakamakon cire tallafin Mai.
Babban mataimakin shugaban hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta ne ya bada wannan tabbacin a karshen mako yayin da yake amsar lambar yabon Titans of Tech (ToT) a jihar Legas.
Garba Danbatta na cewa: “NCC ta fada cewa ba ta shirya kara kudin kiran waya a yanzu sakamakon cire tallafin Mai ba. Irin wannan matakin ya rage ga dukkanin kamfanonin sadarwa su duba abun da za su yanke. Mun tattauna sosai da dukkanin kamfanonin. Don haka wannan ya rage musu su cimma matsaya. Muna tafiyar da aiki da shigo da kowa cikin lamura a NCC. Ba mu yi magana kan karin kudin wayar tarho ba ya zuwa yanzu.”
Dambatta wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar na shiyyar Legas, Mr Yomi Arowosafe, wanda ya amshi lambar yabon gwarzon ‘Pan African Telecoms Operator’ na shekara, yayin da kuma kakakin hukumar Mr Reuben Muoka ya amshi lambar yabon gwarzon jami’in sadarwa na shekara.
Dambatta ya gode wa kamfanin da suka shirya lambar yabon tare da zakule shi hadi da karrama shi. Ya nuna hakan a matsayin matakin da zai kara masa azama a fagen aiki.
Tun da farko da yake jawabi a wajen taron, tsohon gwamnan jihar Legas, Mr Femi Pedro, ya bukaci masu ruwa da tsaki da su ke bayar da fifiko da muhimmanci ga darussan kimiyya, fasaha, injiniyanci da lissafi (STEM) tun daga matakin firemare har zuwa babban matakin karatu.
Kazalika, ya ce, lokaci ya yi da za a karfafi matasa kan hanyoyin dogaro da kai, kirkire-kirkire ta hanyar amfani da fasahar zamani, “Wasu matasa da dama suna ta korafin babu aikin yi, alhali ga hanyoyin da za a iya samun abun yi ta kimiyya ta hanyar kirkire-kirkire.
“Babu bukatar wani ya zauna babu aikin yi a duniyar yau.”