NNPC ta lalata haramtattun matatun mai 69 cikin mako guda

0
159

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, ya ce ya gano haramtattun matatun mai 69 cikin mako ɗaya da ya wuce. 

Wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na Twitter ta ce sun kuma lalata haramtattun bututun man 93 a yankin Neja Delta mai arzikin mai da ke kudu maso kudancin ƙasar.

A 2022, wani rahoto ya ce Najeriya ta yi asarar gangar ɗanyen mai kusan miliyan 65, wanda ya kai fiye da naira tiriliyan biyu sakamakon fasa bututai.

Gwamnatin ƙasar ƙarƙashin Shugaba Muhammadu Buhari ta haɗa kai da jami’an tsaro masu zaman kansu don daƙile matsalar satar man.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here