Ba gudu ba ba da baya kan zanga-zangar tsadar mai – NLC

0
118

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC), ta amince da matsayar da kwamitin ayyuka na kungiyar, da cimma na cewa za su gudanar da zanga-zanga a ranar Laraba 2 ga watan Agustan 2023 a dukkanin fadin kasar nan.

Goyon bayan matsayar na zuwa ne kwanaki biyu bayan kwamitin sulhu da gwamnatin tarayya ta kafa ya kira taron ganawa ta gaggawa da kungiyar Kwadago a Abuja dangane shirinta na shiga zanga-zangar a ranar Laraba din.

Kungiyar ta ce, ta yi nazari da bibiyar halin zamantakewa da na tattalin arziki da irin kuncin da ma’aikata da sauran al’ummar Najeriya ke fuskanta a zaman da ta gudanar a ranar Alhamis, don haka su na goyon bayan matakin.

A jawabin bayan taron, wadda ke dauke da sanya hannun shugaban kungiyar na kasa Comrade Joseph Ajaero, da sakatare janar, Comrade Emmanuel Ugboaja, “Jaddadawa da goyon bayan dukkanin matsayar da zaman CWC ya cimma a ranar 25 ga watan Yuli.”

Ta kara da kagewa kai da fata cewar rashin damuwar gwamnatin tarayya ne ya sanyata kawo wasu tsare-tsaren da suka janyo tashin farashin Mai kuma hakan na nuni da rashin nagartarta wajen gudanar da wakilci.

Ya ce, sun kafa kwamitoci a dukkanin jihohi da za su hada kai da kungiyoyin fararen hula wajen fitowa wannan zanga-zangar adawa da matakan da suka jefa al’ummar Najeriya cikin matsatsin rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here