Amurka ta ce ita da kawayenta na tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, yayin da ta shaida musu cewar hambarar da zababbiyar gwamnatin kasar na iya kawo karshen hadin-kan da ke tsakanin kasashen biyu.Â
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar John Kirby ne ya sanar da haka dangane da halin da ake ciki a Nijar bayan da aka sanar da nada Janar Abdourahmane Tchiane a matsayin sabon shugaban mulkin soja, wanda tuni ya yi jawabi ta kafar talabijin ga jama’ar kasar.
Kirby ya bayyana halin da ake ciki a Nijar a matsayin abin tada hankali, abin daya sashugabannin sojin kasashen ECOWAS da na Amurka da kuma kawayensu suka fara tintibar sojojin ta hanyoyi da dama.
Kakakin gwamnatin ya ce Amurka na Allah wadaida duk wani yunkurin kifar da gwamnati ta hanyar juyin mulki tare da gargadin cewar juyin mulkin zaisanya kasar kawo karshen yarjeniyoyin hadin-kan da ke tsakaninta da Nijar, musamman ta fuskartsaro.Â
Jamhuriyar Nijar wadda kezama kawa ta musamman ga Amurka da manyan kasashen duniya ta fuskar yaki da ta’addanci,na taka rawa sosai a aikin da take yi tare da kasashen yammada zummar cimma muradun da kasashen sukasanya a gaba.
Gwamnatin shugaba Joe Biden na jinjina wa Nijarakan tafarkin demokiradiyar da take dauka kafinwannan lokaci, amma wannan juyin mulkin ka iyakatse tafiya tare da kasashen biyu ke yi saboda kawar da gwamnatin dimokiradiya.Â
Dokar kasar Amurka ta haramta taimaka wa wata kasar waje da ba ta karkashin mulkindemokiradiya, har sai wadda Sakataren Harkokin Wajenta ya bayyana a matsayin wadda take da muhimmanci ga muradun Amurka.
A wannan shekarar kawai, kasar Amurka ta bada taimakon dala miliyan 138 ga Jamhuriyar Nijar domin taimaka wa marasa karfi ta hanyar jin-kai, yayin da tsakanin shekarar 2017 zuwa 2022, Amurkar ta bada dala miliyan 387 ga kasar, baya ga dala miliyan 281 da aka ba ta a matsayintaimako ta fuskar tsaro domin yaki da ta’addancida kuma bunkasa bangaren shari’a.
Yanzu haka akwai sojojin Amurka akalla dubu 1 da 100 a sansanoni guda 2 da ke Nijar, abin da ya saSakatarenTsaron kasar Lloyd Austin ya ce suna sanya ido sosai akan halin da ake ciki a kasar.
A ranar Alhamis din da ta gabata, Majalisar Dattawan Amurka ta amince da nadin Kathleen Fitz Gibbon a matsayin Jakadiyarta a Nijar, kusan shekara guda bayan nada ta da aka yi.Â