Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da daddare

0
145

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da yammacin Litinin.

Mai magana da yawun shugaban, Dele Alake ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da safiyar Litinin.

Ya ce shugaban zai yi jawabin ne da misalin karfe 7:00 na maraice, kodayake babu karin bayani a kan musabbabin jawabin nasa.

Sanarwar ta bukaci kafafen yada labarai su jona da gidan talabijin na kasa (NTA) da gidan rediyon Najeriya domin watsa jawabin kai tsaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here