Yanzu-Yanzu: Jirgin sama yayi hatsari a Legas

0
174
Jirgin Sama
Jirgin Sama

An bayar da rahoton wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a jihar Legas, jaridar Daily News 24 ta kasa tabbatar da musabbabin faduwar jirgin.

Sai dai ‘yan Najeriya da dama sun yi ta yadawa a shafin twitter game da lamarin.

Wani mai amfani da Twitter mai suna @agbajude ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne a Oba Akran. Ya ce “Da alama an yi hatsarin jirgin saman ne a Ikeja babban birnin Legas.

Wasu masu amfani da shafin twitter sun tabbatar da faruwar lamarin.

Bidiyon da Daily News 24 ta samu ya nuna wasu jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Legas a kusa da tarkacen jirgin da ba a tantance ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here