Wasu bata–gari da ake zargin barayi ne sun banka wa wani sashe na tsohuwar kasuwar Gombe wuta cikin dare.
Bayanai sun kiyasta cewa wutar ta jawo wa ’yan kasuwar asara da aka kiyasta ta kai kimanin Naira miliyan 70.
Wutar dai ta tashi ne a layin teloli na kasuwar, inda ta kone kimanin shaguna 20 baya ga kadarorin da aka yi asara.
Daya daga cikin masu shagunan da lamarin ya shafa, Aminu Abdulrahman, ya ce an buga masa waya ne da karfe 1:00 na dare aka sanar da shi iftila’in wutar.
Ya ce ya yi asarar kekunan dinki guda 10 da wasu kayayyaki masu daraja, wadanda aka kiyasta kudinsu ya kai Naira miliyan biyu da dubu 500.
Shi ma Sani Idris, cewa ya yi abin da ya faru abin takaici ne domin an jawo musu asara ba ’yar kadan ba.
Sani Idris, ya kara da cewa shi ma cikin daren aka buga masa waya aka sanar da shi cewa layinsu ya kamata wuta amma suna zargin barayi be suka sa wutar bayan sun saci abin da suka sata a kasuwar.
A cewarsa ya yi asarar kekunan dinki biyar da na saka da sauran kayayyakin da aka kiyasta sun kai Naira 800,000.
Don haka suka yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su kai musu gudunmawa ganin yadda ake fama da rayuwa.
Da yake karin haske kan lamarin, Shugaban Kungiyar Teloli na tsohuwar Kasuwar, Abu Safwan Muhammad Tukur, bayyana kaduwarsa ya yi kan lamarin.
Abu Safwan ya ce mambobinsu da yawa sun tafka asarar dukiya mai dimbin yawa da aka yi kiyasin ta kai Naira miliyan 70.
Daga nan sai ya bukaci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) da ta gaggauta kai musu dauki.
Da muka tuntubi Daraktan Hukumar SEMA na Jihar Gombe, Malam Muhammad Garba, ya tabbatar cewa sun umurci wadanda iftila’in ya afka wa da su rubuta musu, su kuma za su tura wa gwamnati don ganin an taimaka musu.