Faransa ta musanta zargin kai hari a Nijar

0
175

Faransa ta musanta zargin karya dokar sararin samaniya da sojojin mulki a Nijar suka zarge ta da yi.

Sojin Nijar sun zargi Faransa da karya dokar ƙasar ta rufe sararin samaniyarta.

Sojojin Nijar sun zargi Faransa da Æ™awayen ta da Æ™oÆ™arin kuÉ“utar da Æ´an ta’adda da ke tsare, waÉ—anda ake zargi da haifar da rashin tsaro tsawon shekaru takwas.

Amadou Abdraman ne ya bayyana zargin cikin wata sanarwa da ya karanta a talabijin, sai dai babu wata shaidar da ya gabatar game da zargin.

Hakan na zuwa ne lokacin da ake zaman ɗar-ɗar kan zaman da ƙungiyar Ecowas za ta yi a gobe Alhamis, inda za ta tattauna matakan da za ta ɗauka nan gaba, ciki har da matakin soji.

Gwamnatin Faransa ta musanta zargin na sojojin Nijar kan kuÉ“utar da “Æ´an ta’adda” da kuma karya dokar keta sararin samaniyarta.

Lamarin na zuwa ne Æ´an sa’o’i bayan da wani tsohon jagoran Æ´an tawaye ya kafa wata Æ™ungiya a Æ™oÆ™arin mayar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.

Yau Laraba ma an kama É—an jakadiyar Nijar a Faransa, Idrissa Kané, wadda tsohuwar shugabar gidan waya ne na Nijar, inda ake zargin sa da almubazzaranci da dukiyar al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here