ECOWAS ta umarci dakarunta su zama cikin shirn kai yaki Nijar

0
195
ECOWAS-chairman-Bola-Tinubu

Shugabannin ƙasashen ECOWAS sun ba da umarni ga dakarun sojin ƙungiyar su ɗaura ɗamarar kai yaƙi Nijar, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar.

Sanarwar da Omar Aliu Toure, shugaban hukumar ECOWAS , ya karanta bayan taron sirri da suka gudanar, shugabannin ƙungiyar sun ba da umarnin bijiro da dakarun ko-ta-kwana na ECOWAS da yiwuwar tilasta aiki da ƙudurorin ƙungiyar ƙasashen a kan Nijar.

Sun cimma wannan matsaya ce yayin taron gaggawa da suka gudanar ranar Alhamis a Abuja.

Cikin sauƙi, ba za a iya fayyacewa ƙarara, a kan ko umarnin yana nufin dakarun sojin ECOWAS za su auka wa Nijar da yaƙi, ko kuma za su ɗaura ɗamara su zauna cikin shirin yaƙi ba.


Tun da farko, ECOWAS ta bai sojojin da suka yi juyin mulki wa’adin kwana bakwai don su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed da suka hamɓarar daga mulki, ko su fuskanci matakin amfani da ƙarfin soji.

Shugabannin sun ce sun yi nazari kan rahotannin jakadun da suka aika da kuma muhawara cikin tsanaki a kan shawarwarin da manyan hafsoshin tsaron ECOWAS suka bayar da kuma sauran bayanan da hukumar ƙungiyar ƙasashen ta gabatar.

Sun kuma nanata Allah-wadai da juyin mulkin Nijar da kuma ci gaba da tsare Shugaba Bazoum Mohamed.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here