Al-Nassr ta dauki kofin zakarun kasashen larabawa

0
176
Al-Nassr

Cristiano Ronaldo ya dauki kofin Zakarun ƙasashen Larabawa bayan da kungiyarsa ta Al-Nassr ta doke Al-Hilal da ci 2-1.

Dan wasan na ƙasar Portugal ne ya zura duka ƙwallo biyun da ƙungiyar ta ci a ƙarawar.

Wannan shi ne kofi na farko da Ronaldo ya ci tun bayan komawa ƙungiyar a watanni takwas da suka gabata.

Bayan kammala gasar Kofin Duniya ne, Ronaldo ya koma taka-leda a Saudiyya, bayan raba gari da ƙungiyarsa ta Manchester United.

Komawar tsohon ɗan wasan Real Madrid ɗin zuwa Saudiyya ta buɗe ƙofa ga sauran fitattun ‘yan wasan Turai wajen komawa buga gasar ta Saudiyya.

Cikin wannan shekara fitattun ‘yan wasa irin su Karim Benzema da Ngolo Kante da Riyad Mahrez da sauran ‘yan wasan Turai da dama ne suka koma buga gasar ta Saudiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here