Neymar ya amince ya koma Al-Hilal har tsawon kaka biyu

0
311

Dan gaban Paris St-Germain Neymar, mai shekara 31, ya amince da kwantiragin zaman kaka biyu a kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya a kan kudi fam miliyan 138.

Za a yi wa dan tsakiyar Brighton dan kasar Ecuador Moises Caicedo, mai shekara 21, gwajin da ya kamata ayi masa a asibiti a Chelsea tun kafin ma a kamala biyan kudin da aka saye shin a fam miliyan 115.

Tottenham na duba daukar dan gaban Arsenal dan kasar Amurka, Folarin Balogun, bayan barin Harry Kane kungiyar.

Liverpool da Bayern Munich da kuma Paris St-Germain, na sha’awar tayin fam miliyan 32 da Nottingham Forest ta yi wa PSV Eindhoven a kan dan tsakiyar kungiyar Ibrahim Sangare a kakar bana.

Bayern Munich ta ki amincewa da tayin da Manchester United ta yi mata a kann dan wasanta Benjamin Pavard, mai shekara 27.

Manchester United na duba daukar dan tsakiyar Belgium Amadou Onana, dan shekara 21, inda ta ke jiran martananin Everton.

Ajax ta shirya daukar tsohon dan wasan Ingila na ‘yan kasa da shekara 21 Chuba Akpom, daga Middlesbrough a kan kudi fam miliyan 10.

Dan bayan Ingila, Kyle Walker, mai shekara 33, zai sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da Manchester City a wannan makon, inda ya fasa koma wa Bayern Munich. Bayern Munich.

Manchester City na duba yiwuwar daukar dan wasan Crystal Palace dan tsakiyar Faransa Michael Olise, idan har ta gaza cimma matsaya kan daukar dan tsakiyar Brazil Lucas Paqueta.

Ana kyautata tsammanin Liverpool za ta iya biyan abin da Chelsea za ta iya a kan dan wasan Southampton dan kasar Belgium Romeo Lavia.

Juventus na kan tattaunawa da Chelsea a kan daukar dan gaban Belgium Romelu Lukaku, wanda ke son komawa kungiyar.

Dan tsakiyar Netherlands Frenkie de Jong, mai shekara 26, na son ci gaba da zama a Barcelona har karshen rayuwarsa duk da alakar da ya ke da ita da Manchester United.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here