Sojojin Najeriya sun ce suna samun nasara wajen kawar da ‘Yan Bindiga

0
196
Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Babban hafsan Mayakan kasa Lt. Gen. Taoreed Lagbaja da babban hafsan hafsoshin kasar Lt. Gen. Christopher Musa ne suka tabbatar da hakan a Sakkwato lokacin da suka rako tsohon Babban hafsan mayakan kasa Lt. Gen. Faruk Yahaya jihar sa ta haihuwa bayan ajiye aiki.


Tun fara samun matsalolin rashin tsaro a Najeriya gwamnatoci ke cewa suna kokarin shawo kan matsalolin, kuma sukan ce suna samun galaba.

Har yanzu haka batun yake, domin duk da yake ana samun rahotanni kai hare-hare a wasu yankunan Najeriya, rundunar sojin kasar na alfahari da cewa tana samun galaba a yakin da take yi da ayukkan ta’addanci.

Baban hafsan mayakan kasa Lt Gen Taoreed Lagbaja ya ce nasarorin da sojin ke samu yanzu ba su rasa nasaba da kyakkyawan jagoranci da rundunar ta samu a lokacin babban hafsan mayakan da ya ajiye aiki Lt Gen Faruk Yahaya.

Ya ce “yanzu ana samun ‘yan ta’adda wadanda ke tuba su mika wuya, fiye da yadda aka samu a baya, abinda ya farce tsammanin masu lura da lamurra na cikin gida har ma da na kasashen waje.”

Yace “hakama ana samun kyautatuwar zaman lafiya a yankin arewa maso yamma, da kudu maso gabas, arewa ta tsakiya da dukan sannan Najeriya da suke fuskantar matsalolin rashin tsaro”

To sai dai a nashi haujin Babban hafsan hafsoshin Nigeria Lt Gen Christopher Musa na ganin nasarorin da jami’an soji ke samu, baya ga jajircewar su sakamakon kyakkyawan shugabanci da suka samu a baya, akwai goyon bayan da suke samu daga gwamnatocin jihohi, kamar wanda suke samu daga gwamnatin jihar Sakkwato.

To sai dai kuma har yanzu wasu mazauna yankunan karkara na cewa suna fama da matsalolin rashin tsaro, tamkar yadda dan majalisar dokoki naa jiha mai wakiltar mazabar Isa dake gabascin Sakkwato Habibu Halilu Modaci ke cewa.

A dayan bangaren kuma wasu jama’ar yankunan na gabashin Sakkwato sun ce suna samun saukin matsalar ta rashin tsaro.

Duba da yadda matsalar ta ki karewa ne ya sa masana lamurran tsaro da ma daidaikun jama’a da ke lura da lamurran yau da kullum ke kira akan daukar matakai na bai daya a duk da ake da matsalar ko da za’a samu nasarar yaki da ta’addanci ta Isa ko’ina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here