‘Yan ta’adda sun sake kai wasu sabbin hare-hare a Nijar

0
209
Tillaberi-Nijar
Tillaberi-Nijar

Wasu sabbin hare-haren da aka kai a jihar Tilabery ta Jamhuriyar Nijar sa’o’i bayan kisan wasu dakarun tsaro 17 a yankin mai fama da ayyukan ‘yan ta’adda, sun yi sanadin mutuwar gwamman fararen hula, abin da manazarta ke bayyanawa a matsayin girman matsalar tsaron da ta addabi kasashen.

Rahotanni daga jihar Tilabery na cewa tun daga misalin karfe shida na yammacin ranar Talata har zuwa cikin dare da wayewar safiyar Laraba wasu mutane dauke da bindigogi suka afkawa fararen hula a kauyuka da dama na da’irorin Dessa da Mehanna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 31 a cewar wasu majiyoyi.

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya bayyana damuwa akan abubuwan da ke faruwa a ‘yan kwanakin nan.

Ya yi kira ga hukumomi da su duba lamarin da idon basira, sannan ya bukaci al’umma su ba jami’an tsaro hadin kai wajen kokarin yaki da rikicin ta’addancin da ke kara ta’azzara.

A ci gaban aika-aikar da suka kaddamar, ‘yan bindigar wadanda a ke kyuatata zaton mayakan kungiyar reshen IS ne, sun kai farmaki a kauyukan karkarar Anzourou wadanda suka hada da Sarakoira da Theim da Farie da Bissakire da Bangoutande da rugar Bibiyergou inda kuma suka kore kananan dabbobi 555 da shanu 201 to amma ba’a yi asarar rayuwa ko guda ba a cewar wata majiyar ta daban.

Tabarbarewar al’amuran tsaro na daga cikin dalilan da sojoji suka ce sun dogara da su wajen kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

A kan haka shugaban kungiyar agaji ta Action For Humanity, Zirbine Abass ya tunatar da sojojin juyin mulkin alwashin da suka sha kan wannan matsala.

Ya ce “wannan manuniya ce ga CNSP lokacin da suka ayyana matsalar tsaro a jihar Tilabery da sauran jihohi ita ce hujjar da suka fake da ita, muna jiran samun wani sakamako na zahiri.”

“Ko da yake har yanzu ba’a makara ba,” in ji shi, to amma ya ce sun yi zaton samun wani sauyi cikin dan karamin lokaci, kuma gaskiya alamu na nunin har yanzu ana gidan jiya, don haka suke fatan abubuwa za su canza da ganin zaman lafiya ya dawo a Nijar da ma yankin na Sahel.

Kawo yanzu hukumomin tsaron kasar ba su yi bayani ba dangane da wadanan sabbin hare-hare, haka kuma yunkurin jin ta bakin hukumomi a kananan hukumomin da abin ya shafa ya ci tura saboda wasu dalilai masu nasaba da tsarin aiki inji su.

Kafin wadanan hare-hare da suka yi sanadin halaka fararen hula, ma’akaitar tsaron kasar Nijar ta sanar da rasuwar wasu sojoji 17 a kauyen Koutougou kusa da iyakar kasar da Burkina Faso, a wani harin kwanton bauna da ‘yan ta’adda suka kitsa a ranar Talata 15 ga watan nan na Agustan 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here