Tsadar rayuwa: Dan dako ya tsere da kayan abincin wata mata a Abuja

0
153
Dan dako
Dan dako

Wani dan dako mai tura baro ya tsere da kayan abincin wata mata a kasuwar kauyen Kwaita da ke gundumar Kwali a Abuja.

Aminiya ta ruwaito cewa, matar mai suna Rebecca Gbaje ta fashe da kuka yayin da ta nemi dan dakon ta rasa bayan ta tulo masa kayan abinci a baro.

Wakilinmu da ya yi arba da lamarin, ya riski wasu ’yan kasuwar suna jajanta wa matar yayin da kuma wasunsu suka bazama wajen neman dan dakon.

Da take zayyana yadda lamarin ya faru cikin hawaye, Misis Rebecca ta ce ta dora wa dan dakon kayan abinci a baro wadanda suka kunshi awon shinkafa, masara, wake da sauran kayayyaki cefanen abinci domin kai mata su bakin hanya.

Sai dai ta ce ta sanar da dan dakon ya tsahirta ya jira ta kadan a yayin da ta tsaya sayen kifi.

“Bayan na kammala sayen kifin, ina juyawa sai na nemi mai baron nan sama ko kasa na rasa,” inji ta.

Misis Rebecca ta ce ta yi cefanen kayan abinci na akalla N23,300 a kasuwar kauyen.

Bayanai sun ce wadansu da suka tausaya matar da ta ki daina kuka, sun yi mata karo-karon kudi domin ta sake wasu kayan abincin.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here