Hauhawar farashin kayan masarufi ya karu da kashi 31.7% a Najeriya – NBS

0
181

A Najeriya, hauhawar farashin kayayyakin masarufi ta ƙaru zuwa kashi 31.7% a watan Fabrairu, saɓanin kashi 29.90% da aka gani a Janairu, a cewar bayanan da suka fito ranar Juma’a daga cibiyar ƙididdiga ta ƙasar, Nigeria’s Bureau of Statistics (NBS).

Sanarwar ta ce, “Duba da sauyin, hauhawar farashi a Fabrairun 2024 ya nuna ƙaruwar maki kashi 1.80%, idan an kwatanta da Janairun 2024”.

Bayanan sun nuna cewa a ma’aunin shekara bi-da-bi, hauhawar farashi a Najeriya ya kasance da ƙarin kashi 9.79%, idan an kwatanta da kashi 21.91% da aka samu a Fabrairun 2023.

NBS ta ce, “Wannan na nuna cewa hauhawar farashin a matakin shekara bi-da-bi ya ƙaru a Fabrairun 2024, idan aka kwatanta da irin wannan watan a shekarar da ta gabata (wato, Fabrairun 2023)”.

Haka nan kuma, hauhawar farashin kayan abinci a Fabrairu ya kasance 37.92% a matakin shekara bi-da-bi.

Wannan ya kasance da ƙarin kashi 13.57% idan an kwatanta da yadda aka gani a Fabrairun 2023 (24.35%), a cewar rahoton.

Tun a baya, ƙaruwar tsadar rayuwa ta haifar da zanga-zanga a wasu yankunan ƙasar. Sai dai kuma, gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za ta magance waɗannan matsaloli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here