Delta: Dole sai an zakulo wadanda suka kashe jami’an mu – Janar Lagbaja

0
171

Shugaban hafsan sojojin ƙasa Taoreed Lagbaja, ya ce dole sai an zakulo waɗanda suka kashe jami’ansu.

Rundunar sojin Najeriyar ta kuma zargi al’ummar yankin Okuama da ke jihar Delta da ya kasance wurin da aka kashe sojojinsu, da cewa sun koma farfaganda maimakon tsayawa a yi bincike.

Sojojin sun ce kisan da aka yi wa jami’nsu a jihar ta Delta abu ne da aka shirya shi.

Wata sanarwa da darektan yaɗa labaru na sojojin Najeriya, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ya ce maimakon al’umman yankin su taimaka wa sojoji da bayanai da za su kai ga kama waɗanda suka kashe jami’ansu, sun koma yaɗa fargagandar karya da wofi.

Onyeama ya ce abin da suke yi ya nuna cewa kisan sojojin da aka yi wani abu ne da aka shirya tun farko kan dakarun.

Sanarwar ta ce “Kisan wasu sojojin bataliya ta 181ta Amphobious yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya, bayan samun rahoton rikici tsakanin kabilu a yankin Okuama da kuma Okoloba da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu na jihar Delta abin Allah-wadai ne matuka.

Sojoji 16 ne ake zargin wasu matasa sun kashe a jihar ta Delta.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here